Connect with us

RAHOTANNI

Yaki Da Boko Haram: Amfani Da Karfin Soja Ba Shi Ne Mafita Ba – Tony Oyatedor

Published

on

Wata kungiya mai fafutukar ganin an samu zaman lafiya a Nijeriya, ta bayyana cewa yin amfani da jami’an soja wajen dakile ‘yan Boko Haram, ba shi ne mafita wajen dakile ayyukan na Boko Haram ba.

kungiyar mai suna ” Newstime International” ta zo Nijeriya ne domin taimakawa gwamnatin kasar wajen kawo karshen rikice-rikicen da ya addabi kasar.

Kungiyar wacce ta kunshi mabiya Addinin kirista da Musulmi, sun nuna damuwarsu dangane da yadda ake ci gaba da samun rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya.

Da yake jawabi a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu ta kasa NUJ rashen Jihar Kaduna, daya daga cikin shugabanin kungiyar Tony Oyatedor, ya ce, an samar da kungiyar ne domin lalubo hanyar da za a kawo karshen rikice-rikice a fadin Nijeriya, inda ya ce, sun samu damar zama da shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin ba shi shawarwari a kan hanyoyin da gwamnatinsa za ta bi wajen magance ci gaba da afkuwar rikice -rikice a fadin kasar baki daya.

Oyatedor ya ce, ta’addaninci dabi’ace ta jahilci wanda ta fara zama jiki ga wasu ‘yan Nijeriya, inda ya ce, ganin hakan ne ya sanya wakilan kungiyar suka zo Nijeriya domin samar da mafita ga matsalar tsaro a kasar domin zakulo hanya mafita.

Tony Oyatedor, wanda Malamin addinin kirista ne, ya ce, muddin ana bukatar samun zaman lafiya a yankunan kasar nan, sai gwamnatin kasar ta daina yin amfani da karfin Soja, sannan  su kuma ‘yan Nijeriya su hada kansu domin daina nuna wariyar jinsi ko na kabilanci. A cewar sa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: