Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyar IMN Ta Koka Kan Hana Belin El-Zakzaky Zuwa Neman Lafiya

Published

on

Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN), wadda aka fi sani da ‘yan shi’a, ta koka kan halin matsananciyar rashin lafiyar da jagoranta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ke ciki, wanda idan ba a ba shi damar zuwa neman magani ba, yana iya makancewa.

IMN ta bayyana wannan koken nata ne jim kadan bayan wata babbar kotu da ke jihar Kaduna ta ki amincewa da bayar da belin Malamin domin zuwa kasar waje neman magani, bayan da ya halarci zaman kotun a jiya Alhamis.

‘Yan shi’ar sun bayyana hakan ne a cikin wata takarda da suka rabawa manema labarai wadda ke da sa hannun shugaban kwamitin fafutukar neman a saki Zakzaky Abdurrahman Abubakar Yola, sannan kuma sun zargi kotun da kin yin adalci bisa hana wannan beli da ta yi.

“ In za a iya tunawa dai Malamin na tsare ne tun shekara ta 2015 cikin halin rashin lafiya, sakamakon harbin bindigar da ke jikinsa, wanda hakan ta sa ya bukaci kotu ta ba shi damar zuwar kasar waje domin neman lafiyarsa tare da ta matarsa

“ A halin yanzu wannan rashin lafiyar ta yi kamari, har ta kai ga wani sashi na jikinsa ba ya yin aiki, kuma ba ya gani da idonsa guda daya. Bisa wadannan dalilai ne da ma wasu Malamin ke da tsanin bukatar a ba shi damar fita waje domin duba lafiyarsa, kamar yadda takardar ta ce. 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!