Connect with us

WASANNI

Magoya Bayan PSG Sun Ci Mutuncin Neymar

Published

on

Magoyar bayan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German sun zazzagi dan wasan bayan da suka dinga daga wani yanki wanda sukayi rubutun zagi a jikinsa a wasan da kungiyar ta buga na farko a gasar rukuni rukuni ta kasar Faransa. Tun bayan kammala kakar wasan data gabata Neymar dai ya bayyana cewa bayason cigaba da zaman kungiyar shekaru biyu bayan PSG din ta biya fam miliyan 200 ta saye shi daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
Tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona dai itace kungiyar da ake saran dan wasan zai koma wanda hakan yasa magoya bayan kungiyar PSG suke ganin halayyar da dan wasan yake nunawa na kin jinin kungiyar bai kamata ba. Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa PSG zata iya karbar dan wasa Philliph Coutinho da dan wasan baya Nelson Semedo da kuma kudi fam miliyan 50 zuwa 60 idan har Barcelona tayi alkawarin zata iya bayarwa.
A wasan da kungiyar ta PSG ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Nimes dake kasar ta Faransa a wasan farko na kakar wasa ta bana. Magoya bayan kungiyar sun dinga zagin dan wasan sune cewa yabar musu kungiyarsu. Sai dai daman kociyan kungiyar, Thomas Tuchel, ya bayyana cewa bai san halin da dan wasan yake ba kuma daman bai tafi dashi ba a wasan da suka fafata wanda hakan yasa ake ganin danganta ka ta sake yin tsami tsakanin bangarorin biyu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: