Connect with us

TATTAUNAWA

Idan Dan Siyasa Ya Ji Tsoron Allah Zai Rika Yin Komai Daidai, In Ji Wada

Published

on

Alhaji Bashir Wada, jigo ne a siyasar Jihar Kano kuma tsohon dan takarar majalisar tariyya na Karamar Hukumar nassarawa, sannan mai fashin baki kan siyasar kwato wa na kasa hakkinsu. Ya yi bayani kan irin nasarorin da yake gani gwamnatinsu ta samu, a zantawar da ya yi da Sani Tahir Kano, kamar haka:

Da farko masu karatu za su so in takaitaccen tarihin rayuwarka?

Alhamdulillahi, na farko sunana Alhaji  Bashir Wada Sabuwar Singa wanda ake yi wa lakabi da mai sabuwar Singa, kuma ni an haife ni a tsohowar Karama Hukumar Nassarawa tun tana hade da fagge wato Katsina road na tashi na yi makarantar allo kamar yadda aka saba a kofar gidanmu, har zuwa Islamiyya, na yi makarantar firamari  a Dabo daga nann na bar Dabo zuwa Zaria na karasa, a nan sai bosko inda na yi sikandire a nan. Bayan na kammala na dawo gida Kano inda na shiga jami’ar Bayero inda karanta tattali (Economic) ina da (BSC) a wannan bangaren.

Yaushe ne ka tsunduma harkar siyasa?

To! Alhamdulillahi, an fara harkar siyasa tun shekarar (1999)  har zuwa 2003, amma a lokacin ban shige ta sosai ba, amma kuma ana ba da gudummawa sosai da goyan baya, daga bisani bayan an gama gwamnati a 2003 har zuwa 2007 ina a ciki, amma dai nufi ba da muhimmanci a 2015 inda mai girma gwamna ya yi takarar gwamna Jihar Kano Inda a nan ne na ba da Karfi a kan harkar siyasa.

Menene ya ba ka sha’awar shiga siyasa?

Abin da ya ba ni sha’awa shi ne taimaka wa mutane dalilin shiga ta siyasa don inga al’ummar da nake cikinta na taimaka musu ta ko wane fanni wanda dama a kai muke ciki har yanzu da kuma ci gaban addinimu dan naga ina da gudummawar da zan iya bayarwa a wannan fanni na  siyasa, harkar ilimi da sana’o’i.

Ko kana da wani salon siyasa da ya bambanta ka da sauran ‘yan siyasa da muke da su?

Kwarai da gaske na shiga siyasa ne don ci gaban jama’armu ta fannoni da dama. Samar wa da jama’a madogara ta aiki wannan shi ne   abin da ya bambamta mu da sauran ‘yan siyasa da muke da su.

Hon. Me kake so ‘yan siyasa rika sakawa a zukatan su idan sun ci zabe?

Na farko su fara saka tsoran Allah, idan ka saka tsoron Allah za ka yi komai daidai, kuma ban da gaba kamar yanda mai girma gwamna yake yi ka ga ya dauko ayyukan baya yana karasawa, kaga da baya tsoron Allah ai ba zai karasa ba, wannan shi ne abin da ake sa rai ga duk dan siyasa babu gaba ya dauki duk mutanen shi ne.

 Me za ka ce game da nadin kwamishinoni da bai yi ba sai wasu nade-nade?

Alhamdullah nade-naden da duk ake yi tun da aka fara na ga na da me kyau ne don duk wanda aka na da aka tace abin da muke so kenan  a saka mutane wandanda za su taimaki mutane, wannan shi ne daidai tun daga kan shi shuganban ma’aikata da sauran ma’aikata da sakataren gwamnati da suransu duk sun dace da nada su duk, da kuma MD-MD saura kawai a kara zakulo mutane zakakurai kawai.

Ya batun alakar mai girma gwamna da jama’ar Jihar Kano?

Alaka mai kyauce tunda aka yi Jihar Kano mu dai a saninmu ba’a yi gwamnan da yake da alaka mai kyau ga jama’a irinsa ba, gidan mutuwa gidan rashin lafiya, kai wa manyan Kano gaisuwar Sallah, radin suna daurin aure duk sai mai girma gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda za ka ga jama’a yanda suke yin cin-cinrundo suna so wa suna daga masa hannu wanda duk inda ya je bude aiki ko wani sha’ani jama’a ba sa son ya tafi saboda soyayya da kauna da kuma irin ayyukan da ake yi musu.

Ya batun ayyukan da Gwamnatinku ta gada?

Ai ka sosa min inda yake min kaikayi dan ba’a taba gwamnan da ya dauki ayyuka na baya ya dora ba sai Ganduje, mu dauki asibitin Giginyu da na Zoo Road duk ayyukan baya ne amma, ya dora aiki baya ga sabon asibitin kansa wanda duk fadin Afirka babu irin shi, ga tarin ayyuka da yake yi wa mutane ga gadar Zoo Road mai hawa uku, ga gadar sabon gari wanda ba shi ya fara ta ba, amma ya karasata dubi gadar zuwa Madobi, dubi gadar kofar ruwa, kalli titin Dakata zuwa Bela akwai titi kala-kala daga birni har zuwa karkara, ga ba wa matasa ayyukan yi da sauransu.

Mene ne sakonka na karshe?

Sakona na karshe shi ne jama’ar Jihar Kano a kara ba wa mai girma gwamna goyan baya da addu’a a kan ayyukan da ya ke shirin yi wa jama’ar Jihar Kano, sannan mutane mai girma gwamna wanda da za su kara sawa gwamna farin jini a wajen al’umma wannan nauyi da yake kan sa Allah ya ba shi ikon saukewa.

Muna godiya

Ni ma ina godiya kwarai Allah ya saka da Alkhairi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: