Connect with us

WASANNI

Maguire Zai Iya Fin Van Dijk Kokari – Evans

Published

on

Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jonny Evans, ya bayyana cewa sabon dan wasan baya da Manchester United data saya a wannan kakar zai iya fin dan wasan Liverpool, Virgil Van Dijk kokari a gasar firimiya.

Maguire dai yabar kungiyar Leceister City bayan ya shafe shekaru biyu yana bugawa kungiyar wasa inda ya koma Manchester United akan kudi fam miliyan 80, kuma ya zarce kudin da Liberpool ta biya ta dauki Ban Dijk daga Southampton a shekarun baya.

Sai dai Evans, wanda ya lashe gasar Firimiya guda uku a Manchester United ya bayyana cewa nan gaba kadan mutane zasu fahimci cewa tsohuwar kungiyar tasa bata biya kudi a banza ba wajen sayan Maguire.

“Dukkansu manyan ‘yan kwallo ne kuma idan suna buga kwallo suna kwantarwa da ‘yan wasan kungiyarsu hankali saboda haka bazaka iya banbance wanda zaifi wani ba a cikinsu sai nan gaba idan Maguire yayi dadewar da Van Dijk yayi a Liverpool” in ji Evans

Ya cigaba da cewa “Babban abinda yakamata Maguire yayi shine yasan irin aikin da zaiyi a Manchester United kuma yasan dalilin da yasa kungiyar ta kashe nakudan kudade wajen sayansa duk da cewa akwai ‘yan wasan baya da dama a duniya”

Manchester United dai ta sayo Maguire ne domin kara karfi a baya bayan da a kakar wasan data gabata aka zurawa kungiyar kwallaye 54 wanda hakan yasa basu samu damar zuwa kofin zakarun turai ba wanda za’a fara a watan gobe.

A ranar Lahadin data gabata Maguire yafara bugawa Manchester United wasa inda sukayi raga-raga da Chelsea daci 4-0 kuma a wasan Maguire ne ya lashe kyautar dan wasan da yafi kokari sannan a ranar Litinin mai zuwa United din zata fafata wasa na biyu da kungiyar kwallon kafa ta Wolves a wasa na biyu na gasar firimiya.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: