Connect with us

WA'AZIN KIRISTA

Ya Kamata A Kawar Da Kwadayi Tare Da Tabbatar Da Adalci

Published

on

Wurin Karatu – Mika 3:11

“Manyanta suna shari’a domin toshi, priests nata suna koyaswa domin ijara, annabawanta kuma suna duba domin kurdi; duk da wannan sai su jingina ga ubangiji su ce, ubangiji ba shi cikinmu ba? Babu chiwuta da za ta samemu.” (Mika 3:11)

Maganan addini ba maganan wasa bane. Maganan addini, maganar ceto ne. Maganan addini maganan salama ne, kuma magana adalci ne ga kowane irin Bil Adama. In ana magana addini, to ana maganan bautar Ubangiji Allah makaxaici. Ba a maganan addini ba tare da maganan mallamanta ba. Mallaman addinai inji masu iya magana suna cewa: “Mallamai magadan Annabawa ne su.”

To in da gaskiya mallamai magadan Annabawa ne. To ashe, wannan matsayin da mallamai suka gada, ashe babban matsayi ne daga Allah. Mallaman addini, masu gaskiya ne a kowane matakin rayuwa, domin  su misalai ne ga kowa. Annabawa kuma wakilan Ubangiji Allah ne, kuma masu isar da sakon Allah ga bil Adama. Domin da haka, su wakilan gaskiya ne, na Ubangiji Allah ga al’umma.

Amma a wannan ayar da muka karanto a bisa, mun gane da cewa Anabi Mika ya tabbatar mana, mun kuma gane da cewa Annabi Mika ya tabbatar mana da cewa da Annabawa da priests (firstoci) su juya wa Allah baya. Sun koma ga wata rayuwa da ta saba kiran Allah akansu. Watau kira na tsaga gaskiya komi dacinta. Aikin da Allah ya kirawo Annabawa da firstoci (fastoci) sun wofintar da shi. Sun koma ga wata aika-aika da ta saba kiransu da kuma aikin da Allah ya kiraye su.

Anan Annabi Malachi na cewa: ga daliin kiran da Allah Ubangiji ya kirawo Annabawanss da firstoci (fastoci), da cewa:

“Alkawalina yana tare da shi, alkawali na rai da lafiya; na ba su domin shi ji tsoro, ya kwa ji tsorona, ya kwa ga kwarjinin sunana.

Sharia ta gaskiya tana bakinsa, ba a kwa iske rashin adalchi a lebunansa ba; ya tafi tare da ni chikin salama da adalchi, har ya juyadda mutane dayawa ga barin mugunta.

Gama ya kamata lebunan priest su kiyayi ilimi, a kwa nemi Sharia a bakinsa; gama shi Manzon Ubangiji mai-runduna ne”(Malachi 2:5-7).

Abinda Annabi Malachi ya fada itace gaskiyar maganan Allah. Domin Ubangiji Allah ya kirawo Annabawa da priests ko firstoci (fastoci) domin su tsaya a kan gaskiya a kowane lokaci, a kuma ko ina ba tare da jin tsoron kowa ba, domin shi Ubangiji Allah na tare da su.

Amma abin mamaki shine; a lokacin Annabi Mika da Malachi, halaiyan Annabawa da na priests ko firstoci (fastoci) sun sauya gabadaya domin kwadayin abin duniya. Sun juyawa Allah Ubangiji baya tare da maganarsa. Ainihin  kiran da aikin da Allah ya kirawo su, sun juya wa wannan kiran baya sun sauya ta da aikin neman kudi. Sun mayarda aikin Allah na kwadayin abin duniya ba aikin Allah bane kuma!

Malachi ya tabbatar mana da cewa: Shari’a ta gaskiya na samuwa ne daga bakunan firstoci (fastoci) da Annabawan Allah. Amma abin mamaki shine, wannan mutanen sun juya wa Allah baya da kiransu domin kwadayin abin duniya. Annabi Malachi ya cigaba da cewa; “ba a kwa iske rashin adalchi a lebunan sa ba; ya tafi tare da ni chikin salama da adalchi, har ya juyadda mutane dayawa ga barin mugunta.”

Wannan shine kiran da Allah Ubangiji Maitsarki ya kirawo kowane Annabawansa da firstoci a kowane zamani har zuwa yau. Amma zamanin Mika da  Malachi abin ya sauya, zuwa ga aiki neman kudi, ba na neman albarka, da cheto rai da kuma neman shiga Aljanar Allah.

Annabi Malachi ya kara tabatar mana da cewa; kiran da Allah ya yiwa Annabawansa da firistoci(fastoci) domin Jama’a su ilmantu daga wurinsu, da kuma shari’a da gaskiya na lebunansu. Amma abin dai,  “ba nan ne gizo ke saka ba!” Domin Annabi Mika ya tabbatar mana da cewa:

“Manyanta suna shari’a domin toshi, priests nata suna koyaswa domin ijara, Annabawanta kuma suna duba domin kurdi; duk da wannan sai su jingina ga Ubangiji su che, Ubangiji ba shi chikinmu ba? Babu chiwuta da za ta same mu” (Mika 3:11).

A yau halin da aka same su Firstici kenan! Domin da haka, in zamu tuna da zeben shekara dubu biyu da goma sha biyar (2015), mun ji yadda Firstoci ko Fastoci, suka yi ta annabci da cewa Allah Ubangiji ya bayana masu da cewa Goodluck Jonathan zai ci zabe, amma a karshe ya fadi zabe. Kuma a lokacin da Mallamai addini Krista da na Musulunci sun fada ga jaraban karban kudi a wurin ‘Yan siyasa da Gwamnti lokacin domin a zabi wadanda suka basu kudin amma a karshe an sha kunya.

Don Allah Mu ji tsoron Allah mu daina aikata  abin kunya. Don Allah mu girmama kiranmu banda kwadayin abin duniya. Domin da haka Mallaman addinai, mu koma ga Allah mu kuma cigaba a chikin aikin da Allah ya kirawo mu domin mu yi.

 

Shalom!        Shalom!!         Shalom!!!
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: