Connect with us

SIYASA

Gwamnatin Zamfara Ta Ba Mata Tallafin Naira Dubu 20

Published

on

A kokkrin dan Gwamnatin Jihar Zamfara  keyi na ganin ta cika alkawarin da tayi wa matan Jihar Zamfara alokacin kamfen na basu tallafin Jalin Sana’oi ga marasa galihu ,karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad Matawalen Maradun , yanzu haka Matar gwamnan ,Hajiya Aisha Bello Matawale ta jagoranci kaddamar da bada tallafin a Gidan Gwamnati da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Hajiya Aisha Matawale ta bayyana cewa’ wannan tallafin na naira dubu ashirin na masu kananan sana’oi ne ,kuma kowane wata mata dubu daya da dari takwas ne zasu amfana da tallafin a fadin kananan hukumomin jihar ta Zamfara.

Hajiya A’isha Matawalen ta kuma jadda cewa’ tallafin na duk matan jihar Zamfara ne babu banbanci siyasa . kuma fatar mu shine duk wadda ta amfana da wannan tallafin da tayi sana’oi da su ba munbada tallafin yin shagali bane ko anko tallafin na Sana’a da zata taimakin Mata da iyalin su .

Shugabar shirin bada tallafin Hajiya Rabi Ibrahim Shinkafi ta bayyana cewa’ wannan tallafin yanada kwamitoci daban daban dan ganin tallafin yayi aiki inda ya kamata .kuma akwai kwamitn ‘yan sanya Idanu da bin didigi akan yadda ake bada tallafin ,dan ganin bada tallafin bai samu matsala ba.

Hajiya Rabi Ibrahim ta tababtar da cewa’ Duk Wanda aka kama da naiman yima tallafin zagon kasa ba zaiji dadadiba.

Darakta Kudi ta Hajiya Aisha Matawalen Maradun Hajiya Hauwa Hassan ta yi tsokaci ne akan yadda za’atafiyar da kudaden wajan samun nasara kananan sana’oi da Kuma yadda jalin zai habaka zuwa Mayan sana’oi.

Kuma ta yi kira ga wadanda suka samu tallafin da karda suyi amfani dashi wajan bukukuwa ko dinke dinke ,idan suka raini sana’ar su sai sunyi Abu da basu zata ba na cigaban su .

Daya daga cikin wadanda su amfana da tatallafin, Amina Muhammad ta jinjinawa gwamna matawale akan yadda cikin kwanaki sitin da mulkin sa ya cika masu wannan alkawari .dan haka muke rokon Allah ya cika masa burinsa na cigaban jihar Zamfara kuma ya kareshi daga masu naiman kawo masa cikas a mulkinsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!