Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Delta: ’Yan Sanda Sun Damke Barayin Babura

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Delta karkashin CP Adeyinka Adeleke, ta damke barayin babaura a kan titin Ababo da ke cikin karamar hukumar Ikah ta arewa maso yamma ta jihar. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar DSP Onome Onobwakpoyeya, shi ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce, “a ranar 12 ga watan Agusta, tawagar ‘yan sanda da ke yankin Ababo su ka samu bayanan sirri, inda su ka damke wasu mutum biyu wadanda a ke zargin barayin babura ne masu suna Kingsley Onaro dan shekara 25 da kuma Aghulor Udoka mai shekaru 25, a kan hanyar Ababo tare da baburan sata guda biyu, inda daya babur din ta ke da lamba kamar haka FS 135 DT, dayan kuma ba ta da lamba.

“Lokacin da a ka gudanar da bincike a kan wadanda a ke tuhuma, sai Kingsley Onaro ya bayyana yadda su ka shiga gidan mutane sannan su ka yi awon gaba da baburan lokacin da su ke barci. “Ya kuma bayyana cewa, wani mutum mai suna Odogwu Chukwudi dan shekara 41 da haihuwa, shi ne wanda ya ke sayan baburan idan su ka sato tare da wata mata mai suna Blessing Chukwudi ‘yar shekara 40. Ita dai matar ta na sayar da baburan ne bayan an musu takardun jabu. Akwai wata mata mai suna Rita Ifeanyi, ita ta ke yi musu takardun jabu daga ofishin lasisin jihar. “A halin yanzu dai, an samu kwato babura guda 15, inda a ka ijiye su a ofishin ‘yan sandar yankin Owa-Oyibu, an mika wa mutum shida baburansu, sai dai an cire musu lambar baburansu tare da saka wasu na jabu.”

Onobwakpoyeya ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda ta jihar, CP Adeyinka Adeleke ta bayyana cewa, duk wanda ya san an sace masa babur a yankin Owa-Oyibu, to ya garzaya ofishin ‘yan sandar yankin Owa-Oyibu sai ya duba. Ta kuma bayyana cewa, rundunarta za ta cigaba da tsare rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu a jihar baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: