Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Neja: Kotu Ta Daure Mutum Biyu Wata Shida Bisa Satar Kayan Abinci

Published

on

A ranar Talata ce, wata kotu da ke garin Minna ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin dauri a gidan yari na tsawan wata shida, bisa laifin satar kayayyakin abinci. ‘Yan sanda su na tuhumar Babadoko Abdulazeez da kuma Olamide Abdulkadir, da laifuka guda hudu wadanda su ka hada da hada kai domin aikata laifi, shiga shagon mutane ba tare da izini ba, valle wajen ijiya da kuma na sata, wanda ya sava wa sashe na 79, 248, 347 da 288 na dokar fanal kot ta Jihar Neja.

Da ke yanke hukunci, alkali mai shari’a Christiana Barau, ta yanke wa Abdulazeez da Abdulkadir hukuncin bayan ta same su da laifin da a ke tuhumar su da shi. Barau ta bai wa wadanda a ke tuhuma damar biyan tara na naira 80,000 ga kowannan su.

Tun da farko dai, lauya ‘yan sanda mai gabatar da kara, Sajan Stephen Iornem, ya bayyana wa kotu cewa, wata mata mai suna Misis Sadikat Hassan ita ce ta kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sandar yankin Paiko da ke cikin karamar wadanda a ke zargin sun valle mata wurin ijiyar kayayyakin abinci, inda su ka sace buhun shinkafa guda daya, litar man gyada guda 25, katon din yaji guda daya da wasu fakitin tumatur din gwangwani, kudin kayayyakin dai sun kai na naira 32,250. Ta kara bayyana wa kotu cewa, an samu nasarar kwato kayayyakin abincin da su ka sace daga hannun wadanda a ke tuhuma lokacin da a ka gudanar da bincike. Lauyar mai gabatar da kara ta bukaci kotu da ta yanke musu hukunci kamar yadda sashe na 157 dokar manyan laifuka ta tanada.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: