Connect with us

HANTSI

Zaman Aure: Kiyaye Hakkin Juna Shi Ne Gishirin Zama Da Mace Fiye Da Daya

Published

on

Masu karatu barkanmu da sake saduwa a wannan makon a filin naku mai farin jini na Hantsi Leka Gidan Kowa. Kamar yadda muka saba a ko wane mako, a yau ma mun yo muku gagarumar tsaraba game da abin da ya shafi gyaran zamantakewar aure. A wannan zamanin, duk da cewa akwai wasu mata da suka fara fahimtar alfanun kyale miji ya kara aure, har yanzu akwai sauran rina a kaba, saboda wasu sun kasa gane hakan, wani lokaci kuma masu irin wannan tunani ba su da laifi su kadai, abin yakan hada har da laifin miji mai kara aure, saboda gazawarsa wurin yin abin da ya dace a tsakanin uwargida da amarya.

Wasu na ganin auren mace fiye da daya a matsayin shi ne silar rashin samun zaman lafiya, amma abun ba haka yake ba. Wasu sukan ji dadin zama da matarsu ta farko. Ana jin dadin zaman auren mata da yawa ne a lokacin da miji da mata suka kiyaye hakkin juna.

Yana yawan samun rigingimu da matsalolin mabambanta da suke tattare da auren mace fiye da daya ko kuma zaman kishiya da kishiya. Ina kyautata zaton daya daga cikin ma’auratan ko kuma dukkan su ba su bin koyarwar alkur’ani da sunna. Musamman mijin. Musulunci ya koyar da yadda za a yi auren mace fiye da daya wanda ya nuna mana koyi da manzon Allah yadda ya yi da matarsa. Wannan shi ne babban gunshiki ko turba da kowani musulmi ya kamata ya bi wajen koyi da yadda aure yake domin samun nasara.

Auren mace fiye da daya ana ganinsa ne a matsayin cewa, yana amfanar da miji ne fiye da matan, amma a gaskiyan zance yana da matukar wahala ga miji. Musamman wajen daukar dawainiyarsu ta fuskar tufatarwa da ciyarwa da sauran bukatu da kula da yaran.

Ga wasu kadan daga cikin abubuwan da ya sa mata ba su san zama da kishiya.

-Raba soyayya: Babban matsalar da mata suke fuskanta wajen zama da kishiya shi ne, wajen nuna soyayya wanda wannan shi yake kawo rashin jituwa. Soyayya kuwa wani abu ne da ake nunawa a tsakanin jama’a. Ita mace a duk lokacin da mijinta ya karo aure, sai ta dauka ya daina sonta ne wanda wannan ba dai-dai ba ne. A dauki misali da lokacin da uwa ta haifi wani yaro bayan tana da wani za ta nuna soyayyarta ga dukkanin yaran da take da su, tamkar haka abun yake ga namiji, a lokacin da ya karo aure. Maza nagari suna kara aure ne ba wai don ba sa son matayensu na farko ba, domin kuwa idan ba sa son su za su sake su ne su sake wani auren.

-Raba lokaci: Abun da za a raba a zaman kishi shi ne loakcin mijinki. Ko da yana daukan lokaci kadan ne da mijinki, abu ne mai kyau ko mara kyau ya danganta da yanayinki da yadda kike kyautata masa ne.

-Zama da kishiya: Ka da ki yarda ki dauki kishiyarki a matsayin abokiyar adawar ki. Ki yi kokarin tabbatar da cewa kina da kyakkywar alaka da mijinki. Shawara mai amfani daga bakin dan’uwa cewa, rashin tabbas da macen farko shi ne ta tabbatar da cewa mace ta biyu za ta maye gurbinta, a saboda haka ki yi kokarin tabbatar da cewa kin kyautata alaka da mijinki.

Yadda Mata Za Su Magance Kishi

Babban hanyar da za a magance kishi shi ne, ta duba abun da ka dosa. Kishi ne ka sami wani a wurin da kake ganin kai kadai ya kamata a ce ka mallake shi. Idan a alakar ku akwai kishi, ki mayar da hankali wajen kulla alaka mai kyau da mijinki. Ki tabbatar kin jawo hankalinsa a kanki a maimakon ki rika husuma da mijinki. Ki tuna fa Nana Aisha ta yi kishi a kan Manzon Allah wanda har ta taba fasa tangaran saboda da kishi.

Idan kun sami sabani da kishiya, a zauna a tattuana ka da a yi aika-aika domin kaucewa bacin rai.

Aure na baci ne a lokacin wani ya saba wa wani aka kasa yin hakuri da juna, wanda daga karshe saki ya shiga tsakani duk da yake sakin halal ne. A duk lokacin da aka yi auren mace fiye da daya kamar yadda musulunci ya koyar, ba za a taba samun wata matsala ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: