Connect with us

MAKALAR YAU

Wace Gudumawa Kake Bayarwa Wajen Tsaron Jama’arka? II

Published

on

Mai karatu wannan makon ma mun sake dawowa cikin yardar Allah wajen gabatar da wannan shafi mai ilimantarwa game da abubuwan da suka shafi al’amuran yau da kullum, inda kamar kullum muke tattauna muhimman fannoni na rayuwa.

A wannan makon za mu ci gaba ne daga inda muka tsaya a makon da ya gabata, inda muke yin tsokaci game da lamarin nan mai muhimmanci ga rayuwar mu ta yau da kullum, wacce kuma mun sha magana a kanta, wato harkar tsaro, musamman bisa la’akari da ganin cewa harkar sai kara tabarbarewa take yi a nan yankin Arewa maso Yamma, inda a kullum sai sabbin harehare ake kaiwa ga kauyuka.
Kamar yadda muka yi magana a makon da ya gabata, ita wannan harka ta tsaro ba wani abu ne da za a ce za a bar wa gwamnati ita kadai ba, wani abu ne da dole sai kowa ya bayar da tasa gudumawar wajen ganin an kawo karshensa.

Duk da yake aiki ne na gwamnati, amma ita kanta gwamnatin ba za ta samu nasara ba in ba tare da gudumawar jama’a ba, musamman ganin cewa duk masu wannan rashin zaman lafiya suna nan cakude ne a cikin jama’a, don haka dole jama’a su tashi tsaye kowa ya ga wace gudumawa zai bayar wajen kawo karshen wannan abu, a daidaiku ne ko kuma a kungiyance.

Ko ba a fada ba, zaman lafiya ne ginshikin kowane ci gaba, don haka duk inda babu tsaro, to lallai za a tarar da cewa babu wani ci gaba, haka kuma duk inda ake zaman lafiya, to za a rarar da cewa akwai gagarumin ci gaba a wannan wurin.

A irin wannan ne yanzu a halin da muke ciki a wannan yanki namu na Arewa, sakamakon rashin tsaron da ake da shi ya sa komai sai kara komaw baya yake yi, musamman ta fannin tattalin arziki da sauran al’amuran ci gaba da na more rayuwa.

Harkar noma da kiwo, wadanda suke su ne jigon tattalin arzikin wannan yanki, yanzu za mu iya cewa sun koma baya sosai, ta yadda ta kai ma an kwashe wa Fulani shanu an kore su daga inda suke, manoma kuma an hana su zuwa gona ana bi ana karkashewa.

Domin a halin da ake ciki, mawadata masu manyan gidajen gona duk sun rufe su, ba don komai sai don ba za su iya zuwa wurin ba. Irin wadannan abubuwa ne suka hadu suka sanya kusan hankalin kowa, musamman mazauna wannan yankin a tashe yake, ya sa aka dukufa wajen samo hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar daidai gwargwado.

A irin wannan ne wata Cibiya mai kokarin ganin ci gaban Arewa, wato Cibiyar bincike da samar da ci gaba ta Arewa, ‘Arewa Research and Debelopment Project ARDP’,  tare hadin gwiwa da ita Gidauniyar Sardauna da ke Kaduna ta gabatar da wani babban taro a kan haka, wanda kuma taron ya samu halartar masana harkokin tsaro, manyan Malaman Jami’o’i da sauran manyan masu fada a ji na yankin Arewacin kasar nan.

An gabatar da kasidu masu muhimmancin gaske, masu ilimantarwa game da hanyoyin da za a bi wajen shawo kan wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa a yankin, tare da tofa albarkacin baki daga wasu da dama daga wadannan manyan mutane da suka halarci taron.

A wannan taron dai an tattauna hanyoyin da ake jin gwamnati za ta iya bi don shawo kan wannan matsala, amma an fi bayar da muhimmanci wajen hanyoyin da al’umma za su bi don bayar da ta su gudumawar wajen taron kansu da kansu ta hanyar da doka ta yarda ita don su taimaka wa jami’an tsaro a wannan fanni.

A taron dai an kuma tattauna hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin da za a iya fuskanta da kungoyin sa-kai masu taimaka wa jami’an tsaro idan wannan matsala ta kau, musamman duba ga yadda za a yi da su har in Allah ya kawo karshen wannan matsala.

Cikin jawabin da ya gabatar wajen bude wannan taro, Shugaban Cibiyar ta ARDP, Dk Usman Bugaje ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne bisa la’akari da yadda harkar tsaro ta tabarbare a yankin, wanda ya ce idan ba a yi wani kyakkyawan shiri don maganin abin ba, to yankin na Arewa zai zama wani wuri na matattara munanan ayyuka da zaman kashe wando.

Dk Bugaje ya ce, babu wani irin nau’i na bala’in da wannan yanki na Arewa bai gani ba a ’yan shekarun nan a sakamakon tabarbarewar tsaro, inda ake tafka asarar rayuka da dukiyoyin da ba a san adadinsu ba, kuma abin ba ya tsaya ba ne, kullum sai kara ci gaba yake yi.

Dk Bugaje ya kuma bayyana cewa damuwar da suke da ita a tabarbarewar tsaro a yankin ne ya sa suka ga ya wajaba su shirya wannan taro don lalubo hanyoyin da za a bi wajen magance shi. Inda ya ce wannan ne ma ya sa suka zabo masana da manyan Malaman Jami’o’i don tattauna batun.

Game da hanyoyin da za su bi wajen isar da sakamakon wannan taron wajen gwamnati don aiwatarwa kuwa, Dk Bugaje cewa ya yi za su tattara duk abubuwan da aka tattauana a taron, su zauna su fitar da matsaya, wanda wannan matsayar ce za su isar ga gwamnati tare da shawarwarinsu.

Game da ko suna jin idan sun kai wadannan shawarwari nasu, gwamnati za ta aiwatar da su kuwa?

Sai ce, su dai za su yi iyaka nasu abin da za su iya, kuma za su kai masu kamar yadda suka saba yi a baya, ba za su gaji ba, in gwamnatin ta so ta yi aiki da su. A wannan taron dai da muke magana a kai, an karbi rahotonnin yanayin da tsaro ke cikin yankunan Arewacin guda uku, inda Farfesa Ibrahim Tar ya gabatar da na yankin Arewa maso Gabas, sai Mista Chom Bagu da ya gabatar da rahoton yanayin da yankin Arewa ta Tsakiya ke ciki, sannan Dk Abubakar Saddikue Muhammad ya gabatar da na yankin Arewa maso Gabas.

Cikin bayaninsa a wajen gabatar da nasa rahoton daga yankin Arewa maso Gabasa, Farfesa Ibrahim Tar gabatar da jawabi mai sosa zuciya, inda ya bayyana cewa yankin ne ya yi fama da bala’o’i da dama a wadanna shekaru da aka kwashe ana yakI, inda jama’a da dama suka rasa rayukansu, da dama suka jikkata, da dama suka rasa muhallansu.

Farfesa Tar ya ci gaba da bayyana cewa a yankin ba za iya lissafa adadin jama’ar da suka rasa rayukansu ba, baya ga wasu sama da mutum miliyan biyu da dole ta sa suka bar muhallansu, sannan ga matsanciyar yunwar da ake fama da ita.

Ya ci gaba da bayyana cewa yankin ya yi fama da bala’in da ta kai ma duk wani mai tunanin kafa wata masa’anta, ya janye, duk wani mai sana’a ya karye, ita kanta gwamnati ba ta samun daman aiwatar ayyukan more rayuwa, saboda babu damar yin hakan sakamakon hareharen da ake kaiwa a kowane lokaci.

Za mu ci gaba mako mai zuwa in sha Allah. Kamar kullum, za a iya aiko da shawara ko gudumawa ta wannan adireshi [email protected] ko [email protected]
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!