Connect with us

BIDIYO

Gwamnatin Ganduje Ta Nemi Kannywood Ta Dawo Da Motar Da Gwamnatin Shekarau Ta Ba Ta

Published

on

Gwamnatin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta umarci masu sana’ar shirin fim na Kannywood da su dawo da mota kirar Bas, wacce tsohuwar gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, ta taba bai wa kungiyarsu tun a shekara ta 2006, wato shekara 13 da su ka shude.

Wannan bukatar ta fito ne a wata wasika da hukumar tace finafinai karkashin jagorancin Isma’ila Na’abba Afakallahu ta aike wa tsohon sakataren hadaddiyar kungiyar ‘yan fim din Hausa na kasa (MOPPAN), Malam Ahmad S. Alkanawy.

A cikin wasikar, Afakallahu ya yi barazanar a dawo da motar ne cikin awanni 48 ko kuma hukumarsa ta dauki matakin da ya dace.

Haka nan, duk da cewa, Babban Daraktan hukumar tace finafinan ya yi ikirarin cewa, motar kyauta ce gwamnati ta bai wa kungiyar, amma a wani sakin layin ya ambaci motar da “kadarar gwamnati”.

Sai dai kuma bai fayyace ko ita wannan gwamnatin ta Ganduje ta fasa kyautar ne ko akasin haka ba, kafin ta nemi a dawo da motar.

Binciken LEADERSHIP A YAU ya nuna cewa, an dade ba a ganin shugabannin kungiyar jarumai da motar; watakila saboda jimawa da a ka yi a na hawanta har ta gama aiki an jingine ta ko kuma kungiyar ta gaji ta rabu da ita, saboda tsufa.
labarai

Share This

Share this post with your friends!