Connect with us

RIGAR 'YANCI

PDP Ta Mayar Da Martani Kan Harin Da Aka Kai Ma Ta A Kogi

Published

on

Babbar jam’iyyar adawa a jihar Kogi, PDP, ta mayar da martanin game da harin da a ka kai wa taronta na fidda gwani a jihar jiya Laraba, inda ta aika da gargadi mai karfi ga Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, dangane da harin a filin wasa na garin Lokoja a yayin da ta ke tsaka da gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar gwamna da zata tsayar a zaben gwamna da za a gudanar a ranan 16 ga watan Nuwambar wannan shekara.

A wata sanarwa da sakatare na kasa na jam’iyyar, Kola Ologbodiyan ya sanyawa hannu kuma aka rarrabawa Yan jaridu jiya a Lokoja, PDPn tace tada fitina da zubar da jini ko kadan ba zai ceto gwamnan daya gaza da kuma jam’iyyarsa ta APC daga shan kaye ba, ganin cewa jam’iyyar hamayya ta PDP da kuma al’ummar jihar Kogi sun shirya daram Kuma ba gudu ba ja da baya a kudurinsu na ganin sun bi hanyar dimukradiyya don kifar da gwamnatin APC a zaben. da za a gudanar a ranan 16 ga watan Nuwamba. Sanarwan tayi tayi bayani kamar haka” A bayyane yake a zahiri ga kowa cewa gwamna Yahaya Bello ya kasance harbabben bauna ganin cewa al’ummar jihar Kogi sun guje shi da jam’iyyarsa ta APC kuma farin jinin jam’iyyar PDP sai kara karuwa yake yi a kullum a jihar. Shi yasa gwamnan yake neman sanya kafar ungulu don hana jam’iyyar PDP gabatar da dan takarar da zai kara dashi a zaben gwamnan da za a gudanar a watan Nuwamba domin gudun kada ya sha kaye.

Sanarwan taci gaba da cewa” jam’iyyar PDP na tausayawa gwamna Yahaya Bello da jam’iyyarsa ta APC domin kuwa tsarin mu na fitar da dan takara da kuma lashe zaben na watan Nuwamba na Nan daram kuma jam’iyyarmu ta PDP da al’ummar Jihar Kogi sun lashi takobin kawar da gwamnatin zalinci a watan Nuwamba. Sakon mu ga Yahaya Bello da kuma APC ita ce su fara kirga kwanakinsu a ofis, wanda shi ne 27 ga watan janairun 2020, wato ranan da zasu mikawa jam’iyyar PDP mulki” inji sanarwan. Daga nan Kola Ologbodiyan ya ja kunnen gwamna Yahaya a da jam’iyyarsa ta APC dasu guji fushin jama’ar jihar Kogi wadanda tuni sun yake shawarar kwato yancinsu ta hanyar bin tafarkin dimukradiyya a ranan 16 ga watan Nuwamba inda zasu zabi jam’iyyar PDP.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!