Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Delta: Mace Ta Banka Wa Matashi Wuta Kan Bashin Naira 200

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Delta, ta bayyana cewa, ta samu nasarar damke wata mata wacce a ke zargi da banka wa wani matashi wuta, saboda bashin kudi na naira 200. Wata wacce a ke zargin ta na da hannu cikin lamarin, ta gudu, in ji kwamishin ‘yan sandar Jihar Delta, Adeyinka Adeleke. Ta dai banka wa matashin wuta mai suna Sundaya, a yankin Effurun da ke cikin karamar hukumar Uwbie.

Majiyarmu ta ruwaito mana cewa, matar ta bai wa matashin bashin man fetur na naira 200, amma matashin ya kasa biyan matar kudinta. Majiyarmu ta kara da cewa, rikici ya fara barkewa ne tun lokacin da matar ta fara tambayan matashin kudinta na naira 200 wacce ta ke bin bashi. An bayyana cewa, bayan matashin ya ijiye man fetur, sai daya matar ta kasta ashana a inda mamacin ya ijiye man fetur. Mamacin ya mutu tun kafin ya samu ceto daga wurin mutane.

Adeleke ya bayyana cewa, za a gurfanar da matan a gaban kotu, idan an kammala bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!