Connect with us

LABARAI

Buhari Da Atiku: Yau Kotu Za Ta Raba Musu Gardama

Published

on

A yau Laraba, 11 ga Satumba, 2019, ne kotun da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na 2019 za ta raba gardamar da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da dan takarar babban jam’iyyar adawa a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ta hanyar yanke hukunci kan sahihancin zaben ko akasin hakan, wanda hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta gudanar.
Ita dai INEC ta hannun lauyanta, Yunus Ustaz Usman (SAN), ta kafe a kan cewa, ta gudanar da zaben na ranar 23 ga Fabrairu da ya gabata, daidai da tanadin da dokar zaben ta yi kuma masu karar ba za su iya sanya wa a tumbuke wanda ta ayyana a matsayin dan takara ba.
Don haka sai ya nemi kotun da ta yi watsi da karar bakidayanta, saboda rashin tsayayyun hujjoji. Shi ma lauyan Buhari, Wole Olanipekun (SAN), ya nemi kotun ne da ta kori karar, saboda rashin shaidu ingantattu, ya na mai karawa da ambaton sashe na 131 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda bai nemi a saka satifiket din karatu a cikin jerin takardun da a ka wajabta a gabatar, don tsaya wa takara ba.
A nata bangaren ma, jam’iyya mai mulkin kasar ta APC ta hannun lauyanta, Lateef Fagbemi (SAN), cewa ta yi, PDP da Atiku, wadanda ke zargin an tafka magudi a akwatunan zabe 119,973 cikin mazabu 8,809 a sassan kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar, duk da sun kira shaidu 62, amma biyar daga ciki ne kacal su ka ke da alaka da akwatin zabe.
Amma shi kuwa lauyan PDP da Atiku, Leby Uzoukwu (SAN), sun dage ne a kan lallai sai kotu ta yi aiki da sahe na 138 (1) na dokar zabe da ke cewa, dukkan dan takarar da ya gabatar da bayanan karya, to soke zabensa ya kamata a yi.
Ya kara da dogaro da, hukuncin Kotun Koli na shari’a tsakanin Abdulrauf Moddibbo da Mustapha Usman mai lamba SC/790/2019, wanda a ka yanke a ranar 30 ga Yuli, inda ya tabbatar da cewa, cancantar tsaya wa takara ba abu ne wanda sai tun kafin zabe za a tayar da batunsa ba.
Don haka sai ya yi jayayyar cewa, a cikin fom na CF001, wanda Buhari ya gabatar wa INEC ya bayyana satifiket guda uku na kammala firamare, WAEC da shaidar kadet daga makarantar sojoji, amma ya gaza kawo takardun a zahiri.
Don haka sai ya nemi kotun da ta ayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ba shi da cikakkun takardun makaranta, don tsaya wa takardar shugabancin Najeriya. Yanzu dai an zura ido a ji irin hukuncin da kotun za ta yanke yau, bayan shafe tsawon lokaci ta na sauraro da tara hujjojin bangarorin biyu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: