Connect with us

BIDIYO

DA DUMINSA: Hukumar Tace Finafinai Ta Sa ’Yan Sanda Kama Sarkin Wakar Sarkin Kano

Published

on

Rahotanni daga birnin Kano sun tabbatar wa da LEADERSHIP A YAU cewa, hukumar tace finafinai ta jihar Kano qarqashin jagorancin Isma’ila Afakallahu ta sanya rundunar ’yan sanda ta jihar kama Sarkin Walkar Sarkin Kano, wato Malam Naziru M. Ahmad bisa zargin sakin wakoki ba bisa ka’ida ba.

Majiyar LEADERSHIP A YAU ta tabbatar da cewa, jami’an tsaron sun afka gidan Sarkin Wakar ne da yaua Laraba, 11 ga Satumba, 2019, da yammaci, inda su ka gudanar da bincike a cikin gidan bisa zargin cewa ya na gudanar da sutudiyo na kida ba bisa ka’ida ba, amma sai ba su tarar da komai ba.

To, amma bayan hakan sai su ka kuma nuna ma sa takardar shaidar kama shi (warranta of arrest), inda su ka yi awon gaba da shi.

Majiyar tamu ta bayyana cewa, hukumar tace finafinan ta na zargin Sarkin Wakar ne da sakin wasu wakoki guda biyu kimanin shekaru uku da su ka gabata ba tare da samun lasisi daga wajen hukumar ba.

Har zuwa haxa wannan rahoto cikin dare Naziru ya na hannun ’yan sanda, inda a ke tsammanin za a gurfanar da shi a gaban kotu gobe da safe.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda na jihar, don tabbatar da labarin ya ci tura.
labarai

%d bloggers like this: