Connect with us

MANYAN LABARAI

An Sake Kama Mace Bisa Kashe Mijinta Bayan Hukunta Maryam Sanda

Published

on

A ranar Litinin, 27 ga Janiru, 2020, wato ranar da a ka yanke matar nan da kotu ta kama da laifin kashe mijinta, wato Maryam Sanda, Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina ta tabbatar da kama wata mata mai suna Rabi Shamsudeen bisa zargin ta da kashe mijinta a garin Xanjanku da ke yankin qaramar hukumar Malumfashi a jihar ta Katsina.

Jami’in hulxa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ne ya bayyana haka ga menema labarai a Katsina, inda ya ce sun samun nasarar cafke wacce a ke zargin da aikata wannan laifi.

Ya qara da cewa, sun samu rahoto da misalin qarfe huxu na asubahin Litinin xin ne cewa wata mai suna Rabi Shamsudeen ’yar shekarar 19 da ke zaune da maigidanta Shamsudeen Salisu xan shekara 25 da ke qauyen Xanjanku Tasha da ke qaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina ta aikata wannan xanyen aiki.

“Abinda ya faru shi ne maqwabta sun ji kururuwa da ihu lokacin da Shamsudeen ya ke neman taimako a kawo ma sa xauki, kuma alhamdullahi maqwabta su ka je su ka tarar da gidan a kulle ga shi kuma a na jin ihunsa, amma ba damar shiga,” in ji shi.

Jami’in hulxa da jama’a ya qara da cewa, sai maqwabtan su ka yanke shawarar cewa, a haura ta katanga, kuma a ka haura a ka tarar da shi ya fito ya na jan ciki da rauni a cikinsa, an caka ma sa wuqa, jini ya na zuba, sannan a gefe guda kuma sai a ka ga matarsa da wuqa a hannunta, ita ma jini ko’ina a hannunta,” a ta bakin kakakin ’yan sandan.

Kakakin Rundunar ‘yan sanda ya cigaba da cewa, daga nan sai jama’a su ka xauke shi zuwa asibitin Malumfashi, domin ba shi taimakon gaggawa, sai dai Shamsudden Salisu ya rasu a kan hanyar kafin zuwa asibitin.

Ya kuma qara da cewa, bayan sun isa asibitin ne likitoci a babban asibitin Malumfashi su ka tabbatar da rasuwar Shamsudeen Salisu sakamakon caka ma sa wuka da a ke zargin matarsa ta yi ma sa mai suna Rabi.

SP Gambo Isah ya tabbatar da kama Rabi Shamsudeen, wanda ya ce, tuni su ka fara bincike a kan wannan lamari kuma da zarar sun kammala za su miqa ta gaban kuliya manta sabo, domin xaukar matakin da ya da ce da ita a shari’ance.

A jiya ne dai Babbar Kotu da ke zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan shahararriyar shari’an da a ka gudanar kan kashe xan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na qasa, Bello Halliru, wato Bilyaminu Bello Halliru, inda a ka tuhumi matarsa Maryam da yi ma sa kisan gilla ta hanyar soka ma sa wuqa.

A yayin yanke hukunci kan shari’ar, wacce ta xauki hankali, Alqali Yusuf Halilu ya ce ya kotunsa ta kama Maryam Sanda dumu-dumu da laifin kashe mijin nata Bilyaminu, ya na watsi da hujjar da ta bayar cewa, ya fada kan kwalbar Shisha ta soke shi, inda alqalin ya ce, wannan hujja ba komai ba ce, face rainin hankali ga kotun. Don haka ya ce, ta cancanci a rataye ta.

Jin wannan hukunci ya sanya Sanda varkewa da kuka a cikin kotun, inda sai da lauyarta ta rika rarrashinta. Jim kadan bayan tashi daga kotun ne, jami’an tsaro su ka xauke ta zuwa gidan gyaran hali har zuwa lokacin da tabbatar da xaukaka qara ko akasin hakan.

Idan dai za a iya tunawa, an fara wannan shari’a ne shekaru uku da su ka gabata, lokacin da ’yan sanda su ka cafke Maryam tare da gurfanar da ita a Babbar Kotun cikin watan Nuwambar 2017 bisa tuhumar aikata laifuka biyu, waxanda su ka haxa da aikata kisan kai da qoqarin voye gaskiya.

’Yan sandan na Nijeriya dai sun qara da cewa, kisan shiryayye ne, inda ta yi amfani da fasasshiyar kwalba ta aikata shi da misalin qarfe 3:50 na dare. To, amma ita Maryam Sanda ta sha qaryata hakan.

Tuni dai kotu ta sallami mahaifiyarta da sauran waxanda a ka fara tuhuma da haxin baki a cikin lamarin.

Yanzu dai abinda ya rage shi ne, yadda za ta kaya idan Maryam ta xaukaka qara a Kotun Xaukaka Qara da ma Kotun Qoli, idan hakan ta kama a nan gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: