Connect with us

LABARAI

An Yaba Wa Gwamnan Filato Bisa Matakan Baya-bayan Nan Tabbatar Da Tsaro

Published

on

An yaba bisa matakan da Gwamnan jihar Filato, Rt. Hon. Simon Bako Lalong, ya dauka na baya –bayan nan, don kawo karshen satar shanun Fulani da kashe-kashen mutanen da ba su san hawa ba bare sauka a jihar.

Daya daga cikin wadanda rikicin Jos na farko da a ka yi 2001 ya shafa kuma mamba a kungiyar mahauta na jihar Filato, Alhaji Muhammed Sani Standat, ne ya yi wannan yabon a lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa a bisa umurinnin da gwamnan jihar ya bayar na a kama shugabannin Fulanin da masu Unguwanni atsare sai angano wadanda suke da hannu wajen satan shanukan Fulani da kashe kashen mutanen da ba su san hawaba bare sauka a jihar.

Alhaji Sani Sitandat, a tattaunawar da ya yi da wakilumm a Jos a makonnan da ya gabata, ya ce, umarnin da gwamnan ya bayar da a cigaba da tsare masu rike da mudafun iko na al’ummomin yankunan da wadanna kashe-kashen mutane ya afku sai an gano wadanda su ke aikata laifuffukan abu ne da ya dace wanda yakamata da tuntuni an dauka kuma ya yi kira ga sauran gwamnonin jihohin da irin wadannan ayyukan ta’addanci ya ke faruwa da su dauki irin wadannan matakan don kawo karshen aikata miyagun ayyuka a cikin kasar.

Ya kara yaba wa gwamnan bisa nasarorin da gwamnati mai ci yanzu a jihar karkashin jagorancinsa ta samu wajen maido da zaman lafiya da kaunar juna a sakanin al’ummar jihar a cikin dan karamin lokaci dafara janan ragamar mulkin jihar.

Ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnan jihar day a duba dimbin mas’alolin da ke fuskantar ya yan kungiyar wanda yace ya hada karashin wurin yanka dabbobi yaced tunda aka la’lata babbar mayankan dabbobi na jihar a jerin rikice rikecen da akayi a baya suka fuskantar mas’alr karacin wurin yanka dabbobinsu ya bukace shi day a samar masu da sabuwar mayanka da gyera babbar mayankar da ta la’lace don su sami yalwataccen wuraren yanka dabbobinsu. Ya kuma bukaci al’ummar jihar das u jefadda ban bancin siyasa, kabilanci da addini su hakansu su baiwa gwamnan cikakken hadin kai da goyon baya don ya sami karfin gwiwar aiwatar da dimbin ayyukan da ke gabansa cikin nasara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: