Connect with us

RIGAR 'YANCI

Bai Dace A Tura Almajirci Da Sunan Karatun Alkur`ani Ba – Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya bayyana aniyarsa ta cewa ko kadan bai kyautu a ce mutum ya dauki dansa ya kai wani gari almajirci da sunan koyon karatun Alkur’ani ba, bayan kuwa akwai makarantun allo ko dai a kusa da gidansa ko garinsu ko kuma a Unguwarsu, sanin kowa ne wannan ba daidai ba ne, bai kamata ba.

Sarkin Kanon, ya bayyana haka ne a lokacin da yake yin jawabi a wajen wani taron kaddamar da wasu littatafai guda uku, wanda Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya ta Rubuta akan matsalar Aure da kuma Soyayyar aure, wadda aka kaddamar a Gidan Tunawa da Jagoran gwagwarmayar ‘yantar da Talakan Nijeriya, Malam Aminu Kano (Gidan Mumbayya), da ke Unguwar Gwammaja, a ranar Asabar da ta gabata.

Mai martabar ya kara da cewa, abinda ya fi zama wajibi shi ne idan za ka tura yaronka karatu cikin Birni, to dole ne ka tura shi da kayan abubuwan bukatarsa, amma idan ba ka yi haka ba, to kuwa sam ba karatu ka tura shi ba, a cewar Sarkin Kanon.

Har ila yau, ya cigaba da cewa, maganar matsalar barace-barace da wadannan Almajirai ke yi, ko kadan ba laifinsu ba ne; na iyayesu ne. Sannan kuma, bai kamata a rika kama su ba, iyayen nasu ya fi dacewa a rika kamawa, in ji shi.

Haka zalika, mai martaba Sarkin Kanon, ya yi dogon jawabi akan matsalolin aure da saki da kuma matsalar kayan daki, ida ya bayyana cewa kamata ya yi a ce mazaje ne za su rika yi wa matan da suka aura din ire-iren wadannan kayan daki, ba iyayensu ba. “Ko kadan Musulunci bai dora wa iyaye yi wa ‘ya’yansu mata wadannan kayan daki ba, komai kuwa yawan dukiyarsu.

Koda-yake dai, ba kowa ne yake son ire-iren wadannan kalamai nawa ba, sannan kuma ba kowa ne ke iya fahimtarsu ba, amma dai a kwana a tashi wata rana zai fahimta idan lokacin fahimtar tasa ta yi.

A karshe, mai martaba Malam Muhammad Sanusi 11, ya yaba wa Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya, kan wannan aiki nata na rubuta littattafai guda uku tare da shawartar Marubuciyar kan yin bincike mai zurfi, domin amfanin al’ummar duniya baki-daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: