Connect with us

LABARAI

Bakuwar Cuta: Kila Binuwe Ta Kai Gwajin Cutar Kasar Waje

Published

on

A jiya Litinin ce gwamnatin Jihar Benuwe ta bayyana cewa akwai yiwuwar za ta aike da ruwa, yashi, kifi da ganyaye da aka debo daga karamar hukumar Obi ta Jihar zuwa kasashen waje, domin gwajin bakuwar cutar nan da ta bayyana tare da addaban mutanan Jihar.

Kimanin makwanni uku kenan da al’ummun na Oye Obi suna ta fama da wata bakuwar cuta da ta addabi mutanan yankin, wacce a yanzun haka ta kai ga kasha mutane hudu.

Sanata mai wakiltar mazabar Benuwe ta kudu, Abba Moro, ne ya bayyana hakan a zauren majalisar Dattawa a ranar Alhamis, inda ya ce akalla mutane 15 ne ya zuwa yanzun suka mutu a sakamakon bullar bakuwar cutar, inda kuma mutane 104 suke kwance a sakamkon kamuwa da bakuwar cutar.

Da yake Magana da manema labarai ta waya a ranar Litinin, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Sunday Ongbabo, cewa ya yi binciken ruwa da aka gudanar a dakin bincike na Asibitin koyarwa na Jami’ar Enugu bai kammala ba.

Ya ce za sake gudanar da binciken ruwa, yashi, ganyaye da kuma kifin da aka debo daga yankin, ya kara da cewa, akwai yiwuwar bukatar gudanar da binciken a wajen kasar nan.

Ongbabo ya ce, “Muna sa ido sosai a kan duk wadanda suka kamu da bakuwar cutar. Mun yi gwajin cutar zazzabin Lassa da shawara, amma duk sakamkon ya nun aba su ne ba. a yanzun muna jiran sakamakon karshe ne.

Kwamishinan wanda bai bayyana kasar da za a kai binciken ba, cewa dai ya yi, akwai yiwuwar sai mun kai ruwa, yashi, ganyaye da kuma kifin da aka debo daga yankin, bincike a manyan dakunan bincike na wajen kasar nan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: