Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamna Masari Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro A Katsina

Published

on

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya nuna cewar hukumomin tsaro sin taka rawar gani wajen dakile matsalar garkuwa da mutane da yanzu a ke fuskanta a jihar.

Ya hori da cewar sojan Nijeriya sun yi fice wajen aikin dawo da zaman lafiya a nan Afrika da ma duniya ga bakidaya.

Gwamna Masari ya yaba wa yadda sojojin ke nuna jajircewa da kuma nuna kishin kasa wajen tunkarar masu ta’addanci a cikin dazuzzuka.

Kamar yadda ya ce, a na gudanar da bikin ne domin tunawa da sadaukarwar ’yan mazan jiyan wajen kare martabar kasar nan.

Gwamnan ya bayar da tabbacin bayar da goyon baya da hadin kai ga hukumomin tsaro.

Gwamna Aminu Bello Masari da mataimakinshi Mannir Yakubu da Sakataren gwamnati Mustapha Inuwa sun dora Farouk Kaka akan kasancewar Dogon Yaro kuma daga gwamna ya duba farecin girmamawa daga sojojin.

A wani labarin makamancin wannan kuma gwamna Aminu Bello Masari ya bukaci yan sanda su nuna ba sani ba sabo ga duk wanda a ka samu ya na baza labarin karya ta hanyar social media.

Gwamna ya bada umurnin ne lokacin da mataimakin babban sufetan yan sanda AIG Sadik Abubakar Bello ya ziyarcce shi.

Ya bayyana cewar gwamnati na cike da farin ciki dangane da yadda yan sanda suka ruka tafiyar da masu aikata laifuffuka a boye.

Sai dai kuma gwamna ya bukaci yan sanda dasu daina tausayawa yan ta’adda masu garkuwa da jama’a.

Ya bayar da tabbacin shirin gwamnatin shi na cigaba da tallafawa yan sanda su samu su gudanar da aikinsu kamar yadda aka tasara murkushe yan ta’adda.

Tunda da farko mataimakin babban sufetan yan sanda Sadik Abubakar Bello ya bayyana cewar yazo jihar Katsina ne domin samun suna a wannan gundumar.

Ya yabawa gwamna Aminu Bello Masari dangane da yadda yake bada goyon baya ga jami’an ‘yan sanda dake nan jahar.

AIG Sadik Abubakar Bello yace matsalar masu garkuwa da jama’a na cigaba da raguwa.

A wani bangare kwamishinan yan sanda na jahar nan yace suna tsare da wadanda ake zargi na aikata laifi 1256 wadanda ake cigaba da tuhuma a gaban kotu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: