Connect with us

LABARAI

Sanyi Ya Hana Cinikin Lemukan Kwalba A Yobe

Published

on

Wadansu masu siyar da lemukan Kwalba a birnin Damaturu dake jihar Yobe sun koka kan yadda aka samu karancin masu siyan kayayyakinn a wurinsu sakamakon yanayin sanyi da aka shiga.

Yanayin sanyi ne dai yana aukuwa ne tun daga watan Nuwamba har zuwa watan Maris a yankin Sahel da Afrika ta Yamma. Kuma yanayi ne da hazo, iska, da kuma buji ke yawa wanda yake kadowa daga yankunan Sahara ta arewa zuwa kudu da kuma yammacin nahiyar ‘Guinea.’

A wata hira da kamfanin dillancin labaran Nijeriya ta yi da wadansu daga masu siyar da lemukan kwalbar a ranar Laraba a garin Damaturu, sun bayyana kasuwancin a matsayin wani abu da yake kashe musu guiwa a yanzu.

Muhammed Shattima, wanda shima yana siyar da lemukan ya ce masu son siyan lemukan kwalba a halin yanzu sun ragu sosai.

Shima Luka Tizhe ya kara da cewa; a lokacin yanayin zafi, yana da wuya ya samu lokacin sosai ba tare da an zo neman siya ba, inda ya ce a lokacin kwastomomi na musu yawa domin jika makoshinsu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: