Connect with us

WASANNI

Neymar Na Takarar Lashe Gwarzon Janairu A Faransa

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain, Neymar yana cikin ‘yan wasa uku da ke takarar gwarzon dan wasan rukuni-rukuni na kasar Faransa, wato Ligue 1, na watan Janairun daya gabata.

Dan kwallon tawagar Brazil din, yana yin takara ne tare da Moussa Dembele na kungiyar kwallon kafa ta Lyon dan kasar Faransa da kuma dan wasan Reims Yunis Abdelhamid na kasar Morocco

Neymar ya buga wa PSG wasanni biyar a watan Janairu, inda ya ci kwallo shida a raga kuma dan wasan ya ci Monaco kwallo biyu a fafatawar da suka yi ranar 12 ga watan Janairu, sannan ya kara cin Monaco daya a 4-1 da suka yi nasara ranar 15 ga watan Janairu.

Haka kuma shi ne ya zura kwallo biyun da PSG ta doke Lille a gasar ta Ligue 1 ranar 26 ga watan Janairu wanda wadannan kwallaye suna daya daga cikin abubuwan da suka sanya ya shiga cikin jerin ‘yan wasan uku da zasu iya lashe kyautar

Kungiyar Paris St Germain tana ta daya a kan teburin French Ligue 1 da maki 61, bayan karawar mako na 24 sai Olympikue Marseille ce a mataki na biyu da maki 49, sai Stade Rennais ta uku da maki 41 kuma Paris Saint-Germain za ta ziyarci Amiens SC a wasan mako na 25 a gasar ta Ligue1.

Ba wannan ne karo na farko ba da dan wasan yake shiga cikin sahun ‘yan wasan da suke takarar lashe kyautar gwarzon dan wasa na wata-wata da hukumar kwallon kafar kasar take bayarwa saboda a baya ya lashe kyautar da yawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: