Connect with us

LABARAI

Sarkin Musulmi Ya Nemi A Dauki Matakai Wajen Magance Matsalar Tsaro

Published

on

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammed Sa’ad Abubakar, ya nemi shugabanni su dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da zaman lafiya a kasarnan.

Sarki Musulmi ya bayyana haka ne a yayin da yake na shi jawabin a garin Osogbo ta jihar Osun a ranar Laraba a taron da gwamnan jihar ya kira Sarakunan gargajiya domin tattaunawa yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya baki daya.

Sarkin Musulmi ya nuna bukatarsa na ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai wajen tabbatarv da tsaro a kasarnan. Sarkin ya kuma nemi a shugabanni su rika nuna kyakkyawan shugabanci, inda ya ce shugabanci na gari da nuna adalci suna daga cikin abubuwan da suke tabbatar da zaman lafiya.

Sannan ya bukaci ‘yan kasa da su tashi tsaye su yi magana da murya daya ciki gaskiya da tsoro Allah wajen tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya.

Har wala yau ya nemi Iyaye da su rika yiwa ‘ya’yansu da suke tasowa tarbiyyar da ta dace, inda ya ce hakan ne zai magance matsalolin rashi tarbiyya a cikin al’umma.

Sarkin Musulmi ya ce yanzu lokaci ya yi da kowa zai rika bunkasa zaman lafiya, hadin kai musamman idan aka yi duba da halin da kasar ta fada.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: