Connect with us

JAKAR MAGORI

’Yan Fashi Biyar Sun Shiga Hannun ’Yan Sanda A Akwa Ibom

Published

on

A ranar Asabar ce, rundunar ‘yan sandar Jihar Akwa Ibom, ta bayyana cewa ta samu nasarar damke ‘yan fashi guda biyar, wadanda suke da hannu wajen fashi da makamin da a ke kaiwa a garin Uyo.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, SP Odiko Macdon, shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a ranar Asabar.

A cewar Macdon, makon da ta gabata, wasu ‘yan fashi sun farmaki mazauna wannan garin, inda suka kwace wa mutane kudadensu da wasu kayayyakinsu.

“A makon da ta gabata ce, rundunar ‘yan sandar Jihar Akwa Ibom, ta samu rahoton cewa, wasu ‘yan fashi sun farmaki mutane a kan titin Akwa Ibomites kusa da Aka da Udo Umana da Etuk da kuma Nwaniba, da misalin karfe shida na yamma da karfe bakwai na yamma.

“Lamarin ya yi kamari ne sakamakon babu wanda ya kira ‘yan sanda, inda a wannan rana ‘yan fashi suka ci karansu babu babbaka.

“Lokacin da lamarin ya faru, sai rundunar ‘yan sanda suka dauki mataki zakulo wadanda suke da hannu wajen gudanar da wannan fashi. Sakamakon haka ne ‘yan sanda suka samu nasarar damke Ubong I. Asukuo da Unwana E. Etim da Sabiour U. Oso da Idongesit E. Okon da kuma Sunday E. Edet, dukkan su sun fito ne daga yankunan Mbikpong Ikot Edim da Ikot Udo Ekop da ke cikin karamar hukumar Ibesikpo Asutan.

“Lokacin da aka gudanar da bincike, sun tabbatar da cewa su ‘yan kungiyar asire ne wadanda suka addabi yankin Uyo. “Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa, wadannan ba su kadai ba ne, ta na kokarin farautan sanran ‘yan fashin,” in ji Macdon.

Ya bukaci mazauna yankin su taimaka wa jami’an tsaro wajen samun nasarar damke sauran ‘yan fashi da makami. Macdon ya gargadi ‘yan fashi da su daina aikata wannan mummunan aiki ko kuma su fuskanci hukunci a gaban shari’a. ya kuma tunatar da ‘yan acaba wadanda suke aiki da baburansu a yankin Uyo da Eketa, su dunga aiki a tsakanin karfe shida na safe sannan su rufe karfe shida na dare. Ya ce, wannan doka zai kawo tsaro a wannan yankin. “Rundunar ‘yan sanda za ta saka kafan wado daya da duk wanda ya sabawa wannan doka, domin za ta kama shi sannan ta gurfanar da shi a gaban kuliya. “Wannan doka ta shafi har da jami’an tsaro,” in ji shi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: