Connect with us

LABARAI

Kawar Da Poliyo: Gwamnatin Katsina Ta Nemi Masu Ruwa Da Tsaki Su Kokarta

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta bukaci masu ruwa da tsaki a harkar kawar da cutar Poliyo da su tabbatar da ganin sun sauke nauyin da ke kansu, musamman Hukumar cibiyar dakuna shan magani ta jihar, Sarakunan Gargajiya da sauran wadanda suka damu lafiyar al’ummar su.

Mataimakin Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu ne ya yi wannan kira ranar Talata da gabata a lokacin da yake jagorantar babban taron Hukumar da ke da alhakin gudanar da allurar rigafin sha inna, don kawar da cutar gaba daya, wanda za a fara a karo na 61.

Daga nan Mataimakin Gwamnan ya yi kira ga Hukumomi da cibiyoyin samar da agajin kiwon lafiya wajen tabbatar da kowa ya bayar da tasa gudumawar wajen kawar da wannan cuta gaba daya.

Duk wannan bayani yana kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba Mataimakin Gwamnan shawara kan harkokin yada labara, Alhaji Ibrahim Musa Kalla ya sanya wa hannu ya raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa Mataimakin Gwamnan ya kuma yi kira ga Shugabannin Kananan Hukumomi su hada hannu da shugabannin cibiyoyin dakunan shan magani na wurarensu wajen ganin an yi duk abin da za a yi don kawar da wannan cuta ta shan inna gaba daya a jihar.

Alhaji Mannir Yakubu ya kuma yi kira ga Sarakunan gargajiya kan su sauke nauyin da ke kansu wajen yin kira, tare da tsawatarwa, da kuma nuna wa wadanda ba sa son bayar da ’ya’yan don wannan allurar rigakafi irin hadarin da ke tattare da yin hakan.

A karshe Mataimakin Gwamnan ya gode wa ma’aikatar lafiya ta jihar, cibiyar dakunan shan magani, Sarakunan gargajiya, Malaman addini da ’yan jarida bisa gudumawarsu wajen yakar zazzabin Lassa a jihar, inda ya tabbatar da shirin gwamnati wajen yakar wannan cuta a ko da wane lokaci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: