Connect with us

Da dimi-diminsa

Da Dimi-diminsa: Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Abba Kyari Ya Kamu Da Coronavirus

Published

on

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar #Coronavirus.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, hukumar NCDC ta sanar da shugaba Buhari cewa ba ya dauke da cutar a yau Talata, bayan gwajin da aka yi masa a jiya don tabbatarwa.

Majiyar ta ci gaba da cewa, an yi wa shugaba Buhari gwajin ne bayan da Shugaban Ma’aikatansa Abba Kyari ya kamu da cutar.

Rahotannin sun ce, Abba Kyari ya je Kasar Jamus a ranar 7 ga watan Maris din shekarar nan, inda ya tattauna da wakilan kamfanin #Siemens a birnin Munich dangane da batun wutar lantarkin Nijeriya.

Sai da ya yi mako guda a can Jamus din kafin ya dawo, sai dai bayan dawowarsa a ranar 14 ga watan Maris sam bai nuna wata alama ta kamuwa da cutar ba.

Majiyar ta mu ta ce, a ranar Lahadi 15 ga watan Maris Abba Kyari ya halarci taruka mabambanta ciki har da taron yadda za a shawo kan cutar #Coronavirus a Nijeriya. Daga nan ne ya fara mugun tari. Daga nan ya je ya yi gwaji sannan ya killace kansa. Wanda a jiya Litinin aka tabbatar da yana dauke da cutar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: