Connect with us

LABARAI

Shugaban NIS Ya Tabbatar Da Cika Umurnin Gwamnati Na Rufe Iyakokin Kasa

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Muhammad Babandede ya bayar da umurci yin cikken aiki da umurnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na dakatar da sufurin jiragen sama a bangaren kasashen waje da kuma rufe iyakokin kasa na kan-tudu domin kiyaye rayuka da koshin lafiyar ‘Yan Nijeriya da sauran baki da ke cikin kasa daga annobar cutar sarkewar numfashi (COVID-19).

Umurnin na Babandede ya zo ne nan take bayan gwamnati ta bayar da umurnin rufe iyakokin kasa na kan-tudu da kuma bukatar rufe tashoshin jiragen sama da na ruwa da ke zama mashigin kasa domin dakile bazuwar annobar cutar sarkewar numfashi wacce za a iya shawo kanta ta hanyar kara sanya ido a kai-komon jama’a, a tsakanin iyakokin kasa da kuma lura da wadanda suka je kasashen waje suka dawo da ke bukatar a kebe su don gano ko sun yi guzurin cutar zuwa cikin kasa.

Sanarwar manema labarai da Jami’in yada labaran NIS, DCI Sunday James ya fitar a madadin shugaban hukumar ta yi bayanin cewa hukumar ba za ta yi kasa-gwiwa ba wajen tabbatar da kula sosai da kai-komon jama’a a wannan lokaci na jarabta ga kasarmu domin bayar da gagarumar gudunmawa ga kiyaye koshin lafiyar ‘yan kasa.

Sakamakon umurnin na gwamnatin tarayya, NIS ta umurci daukacin jami’anta da ke tashoshin jiragen sama da na ruwa da iyakokin kasa na kan-tudu su tabbatar da rufe iyakokin a tsakanin wa’adin da aka diba.

Shugaban NIS, Muhammad Babandede ya tabbatar wa da ‘Yan Nijeriya dukufar da hukumarsa ta yi wajen yin aiki daidai da yadda ake yi a kasashen duniya da suka ci gaba wajen kula da shige da ficen kasa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: