Connect with us

LABARAI

Coronavirus: Gwamnatin Bauchi Ta Umarci Rufe Kasuwanni Don Kariya Daga Annobar

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki matakin rufe dukkanin kasuwannin da suke jihar tare da neman jama’an jihar da su daina cinkoso domin kariyan kai daga cutar Coronavirus mai hanzarin kisan jama’a.

Da yake ganawa da ‘yan jarida a jiya, mataimakin gwamnan jihar Sanata Baba Telah, ya shaida cewar daukar matakin ya zama tilas lura da yanda cutar take da hatsarin gaske da hanzarin kamuwa, yana mai fadin cewar ba wai sun dauki matakin ne domin musguna wa jama’a ba illa domin su kiyaye musu rayuka da lafiya.
Sanata Baba Telah sai ya ce ‘yan sanda za su yi kokarin tabbatar da kowa ya bi umurnin da gwamnatin ta fitar domin kiyayewa.
“A bisa daukan matakai don kare yaduwar cutar a jihar Bauchi. Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bada umurnin cewa, a rufe dukkanin kasuwannin da suke jihar. Illa kawai ban da wuraren saida kayan abinci, da kayan magunguna, da kuma manya-manyan shaguna (Supermarkets) tare da gidajen Mai wadannan sune kawai za a bari a bude,”
Ya kuma ce, sun umurci jami’an tsaro na ‘yan sanda domin tabbatar da jama’an jihar sun bi wannan umurnin da gwamnatin ta sanya a kansu.
“An kafa wannan dokar ne ba don a musguna wa mutane ko a takura musu ba, a’a an yi ne domin kariya daga annobar nan da ta samemu; dole ne mu yi dan hakurin ‘yan kwanaki domin kiyayewa,” A cewar shi.
Sanata Tela, ya ce gwamnatin ta dauki dukkanin matakan da suka dace tare da sake maguden kudade domin sayowa da nemo dukkanin abubuwan da suka dace domin dakile yaduwar cutar a tsakanin jama’a.
Daga bisani ya bukaci masu sana’ar kabu-kabu na mota da su daina cinkoson fasinjoji domin kiyaye kai daga cutar, tare da sayen sinadarin wanke hannaye domin disa wa fasinjoji.
Daga bisani mataimakin gwamnan ya bukaci jama’an jihar da su rungumi dabi’ar wanke hannaye da tsafta domin kiyaye kawuka daga cutar, sai ya nemi jama’a da su taya da addu’a domin kawo karshen cutar.
Da yake bayyana halin da ake ciki yanzu haka a jihar, ya ce ba ya ga gwamna Bala babu wani da aka tabbatar na dauke da cutar zuwa yanzu, “Daga cikin wadanda aka dibi jininsu domin gwaji su mutum 28 kawo yanzu gwamnan jihar Bauchi ne kawai aka tabbatar da yana dauke da cutar, mutum takwas daga cikin makusantansa an gwadasu ba su dauke da cutar. yanzu muna jiran sakamakon sauran mutanen daga cikin wadanda aka dibi jininsu ne,” A cewar mataimakin gwamnan jihar.
A cewar shi sun dauki matakai na gaggawa da shirin ko-ta-kwana kan cutar; “Mun je mun duba asibitin koyarwa ta ATBUTH domin ware wuri na musamman don shirin ko-ta-kwana koda cutar za ta yi tsanani; ta yanda idan aka samu mutum da ya kamu za a iya kula da shi a nan jihar.
“Kamar yanda kowa ya sani kawo yanzu mutum daya ne wanda aka tabbatar yana dauke da cutar ta Coronavirus wanda kuma shine gwamnan jihar Bauchi, kawo yanzu yana amsar magani kuma tabbas babu wani alamar ciwon nan da ya bayyana a jikinsa. Amma dai a bisa daukar mataki, gwamnan na killace kuma yana amsar magani,” A cewar mataimakin gwamnan.
Ya kara da cewa, sun kuma kebe wuri na musamman domin shirin ko-ta-kwana a asibitin Azare da Misau domin shirin koda za a samu mai dauke da cutar domin bayar da kula na gaggawa, “Mun kuma kawo maganguna koda za a bukacesu. Shi kuma kayyakin da ake amfani da su domin tantance mutum na dauke da cutar ko babu shi ma mai alhakin kawowa na kan nashi kokari, amma hukumar dakile yaduwar cutuka da ta ke da alhakin tabbatar da shin wannan kayan gwajin za a iya amfani da shi, idan ta tabbatar ma na za mu sayo,” A fadin shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: