Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Xi Jinping Ya Yi Kira Da A Dauki Dukkanin Matakan Yaki Da Cutar COVID-19 A Duk Duniya Baki Daya

Published

on

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a dauki dukkanin matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a duk duniya baki daya. Yana mai cewa abu ne mai muhimmanci ga kasashen duniya, su karfafa kwarin gwiwarsu, su hada kai, tare da aiki tare, domin dakile wannan annoba cikin hadin gwiwa.
Xi Jinping ya bayyana hakan ne a yau Alhamis da dare din nan bisa agogon Beijing, yayin da yake halartar taron kolin G20 na musamman kan batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ta kafar bidiyo. Ya ce Sin ta karbi tallafi da karfafa gwiwa daga sassan duniya daban daban, a lokacin da take tsaka da fuskantar mawuyacin hali na yaki da cutar ta COVID-19.
Sannan shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara karfin samar da magunguna, da kayayyakin masarufi, da na kandagarkin cutar ga kasuwannin duniya, za ta kuma tsaya tsayin daka a fannin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, tare da kyautata yanayin kasuwanci a kasar, da habaka shigowa da kayayyaki daga ketare, don samar da gudummawarta ta gani ga kiyaye tattalin arzikin duniya.
Har ila yau, ya jaddada cewa, cutar ta haifar da munanan illoli ga ayyukan samar da kayayyaki a duniya, don haka kamata ya yi kasa da kasa su hada kansu wajen daukar managartan matakai daga manyan fannoni don hana tabarbarewar tattalin arzikin duniya.
Baya ga haka, ya kuma yi kira ga kasashen G20 da su dauki matakai na bai daya, su rage kudin kwastam, da kawar da shingayen ciniki, don farfado da tattalin arzikin duniya.
Kasar Saudiyya ce ta dauki nauyin shirya taron, kuma an gudanar taron ne ta yanar gizo. Kasashe mambobin G20, da kasashe baki, da kuma jami’an kungiyoyin kasa da kasa masu ruwa da tsaki sun halarci taron. Wannan ne karon farko da G20 ta gudanar da taron shugabanninta ta yanar gizo, haka kuma karo na farko da shugaban kasar Sin ya halarci babban taron kasa da kasa tun bayan barkewar cutar. (Masu Fassarawa: Lubabatu Lei, Saminu Alhassan)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: