Jam’iyyar PDP ta ce subul da baka da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya yi a wajen kaddamar da takararsa a Jihar Filato, kan nemawa PDP albarka a maimakon APC, wata alama ce ta nasara.
PDP ta ce wannam wata ‘yar manuniya ce ta cewar jam’iyyar ce za ta yi nasara a babban zaben 2023.
- Yawan Kayayyakin Da Masana’antu Sin Suka Samar Ya Karu Da Kaso 5 A Watan Oktoba
- Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Afirka Ta Kudu Da Na Kasar Senegal
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ne, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce nasara na tare da su ba jam’iyya mai mulki ba.
Hakazalika, ya ce yana da kyau APC ta fahimci cewar ‘yan Nijeriya ba sa muradin sauraren dukkan wani jawabi daga bakin dan takararta.
“Dan takarar APC ya fi kyau ya mayar da hankali kan bayanan bogi da ya bayar wanda suka shafi iliminsa, shekaru da kuma tarin aikin da ya yi ga ‘yan Nijeriya a yanzu.
“Yi wa PDP addu’a wata alama ce ta nasara, wanda Asiwaju Tinubu da yana da kwarin guiwa da ya nemi gafarar ‘yan Nijeriya ya hakura da neman takara,” kamar yadda ya bayyana.