A ci gaba da tuntubar kungiyoyi da shugabannin Addinai da tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma daya daga cikin masu takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Sanata Ahmad Rufa’i Sani Yarima, yake yi.
Sanata Yarima ya ziyarci babban malamin Coci kuma shugaban gidauniyar wanzar da zaman lafiya, John Cardinal O. Onaiyekan a gidansa da ke Abuja don sanar da shi kudurinsa na takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC da neman tabarraki da addu’a da tabbatar da niyyarsa ta samar da zaman lafiya a Nijeriya.
- Babu wata Yarjejeniya Da Aka Gindaya Cewa Za A Ba Tinubu Shugaban Kasa Bayan Buhari -Yerima
- 2023: Yarima Ne Kadai Zai Iya Dorawa Da Irin Nasarar Da Buhari Ya Samu A Mulki —Olumide
Yarima ya ce, kirkiro ma’aikatar kula da harkokin Addinai a Nijeriya zai taimaka wurin samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai a Nijeriya
Ahmad Yerima ya tabbatar da cewa a burinsa na ceto Nijeriya da kuma matsayinsa na dan Jam’iyyar APC mai biyayya, zai goyi bayan duk wanda Jam’iyyar ta tsayar a matsayin dan takararta ko da kuwa shi bai samu nasara zama dan takarar Jam’iyyar ba.
Sanata Yarima ya ce dukda cewa mai alfarma Sarkin Musulmi na jagorantar majalisar addinai kuma suna kokari, dukda haka akwai bukatar a samu fiye da haka, ” Yana da kyau a samu ma’aikata ta musanman da zata kula da harkokin addinai da zata kula da lamuran Musulmi da Kiristoci a Nijeriya, wannan na cikin kunshin kudurinmu cikin ikon Allah da zarar mun yi nasara a 2023” Cewar Yarima.
A nasa jawabin babban malamin cocin, John Cardinal Onaiyekan, ya ce kowane dan adam yana iya bakin kokarinsa kan neman bukatarsa sai da kuma Allah ne mafi sanin waye zai zama shugban Nijeriya a gobe cikin dubban maza da mata da muke da su.
Bishop Onaiyekan ya ce, “Zan ci gaba da yi maka Addu’a da neman Allah ya ci gaba da shiga lamuranka a cikin wannan gwagwarmaya”.
Onaiyekan, ya bukaci sauran jagororin Siyasa da masu muradin tsayawa takara da su yi koyi da salon Ahmad Sani Yarima, ta yadda za su samu hasken damar shugabancin Nijeriya cikin dafawar ubangiji.
A yayin ziyarar Sanata Yerima yana tare da dawagar yakin neman zabensa.