Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa babu gudu, ba ja da baya wajen bayyana sakamakon zabe ta na’ura kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.
Jami’in ilmantar da masu zabe na hukumar, Mista Festus Okoye shi ya bayyana hakan a cikin makon da ya gabata lokacin da yake musanta rahoton wasu jaridu da ke cewa hukumar ba za ta bayyana sakamakon zaben 2023 ta na’ura ba duk da samar da na’urar bayyana sakamakon zaben da aka yi.
Okoye ya kara da cewa bayyana sakamakon zabe ta na’ura ya zama wajibi a zaben 2023, wanda shi ne zai bai wa ‘yan Nijeriya gwarin gwiwan gudanar da sahihin zabe da hukumar INEC take kokarin yi kamar yadda ta fitar a jaddawalinta.
A cewarsa, ratotannin da wasu jaridu suka wallafa na cewa hukumar ba za ta bayyana sakamakon zabe ta na’ura ba sun saba wa dokar zabe ta 2022.
Ya ce, “Hukumar zabe tana jan kunnen jaridun da suka baga wannan labarin na ba za ta yi amfani da na’urar bayyana sakamakon zabe ba, wannan ba gaskiya ba ne.
“Shirin bayyana sakamakon zabe a na’ura yana nan daram kamar yadda aka gudanar a zaben gwamnan Jihar Ekiti da Osun. Babu damar yin zabe ba tare da bayyana sakamako ta na’ura ba ciki har da babban zaben 2023.
“Sashi na 60, 62 da kuma 64 na dokar zabe ta 2022 su suka samar da bayyana zabe ta na’ura.
“Muna kira da ‘yan Nijeriya su tabbatar da cewa hukumar za ta bayyana sakamakon zabe ta na’ura, sannan su yi watsi da rahoton da ke cewa hukumar ba za ta yi amfani da na’urar bayyana sakamakon zabe ta na’ura ba.”