Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana cewa a shirye take ta mara wa duk wani dan takarar kujerar shugabancin kasar a zaben 2023 baya bisa cancanta.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi lokacin taron kaddamar da wani littaci da kungiya matasan arewa masu muradin masar da kyakkyawan shugabanci ta gudana a Kaduna.
- Kwastam Ta Damke Mazakutar Jaki 7000 Da Miyagun Kwayoyi A Legas
- An Shirya Tattaunawar Tiangong Tsakanin ‘Yan Sama Jannatin Sin Da Matasan Afirka Cikin Nasara
Farfesa Ango wanda shi ne shugaban taron, ya nuni da cewa arewa za ta mara wa duk wani dan takarar shugaban kasa baya ne kawai bisa la’akari da cancantarsa, da zai iya yin shugabanci cikin gaskiya, kwarewa, tausayi da tsoron Allah.
Ya tabbatar da cewa yankin zai goyi bayan dan takarar da baya neman cin gajiyar dabarun amfani da bambancin kabilanci da addini na yankin.
Farfesa Ango ya ci gaba da cewa, arewa ba za ta goyi bayan dan takarar da ya kasa gamsuwar da al’ummar cewa zai iya inganta harkokin mulki da kuma mutuncin shugabanni.
Ya ce yankin arewa za ta shiga harkokin siyasa daidai bakin gwargwado da kuma mutunta sauran ‘yan Nijeriya masu mutunta su.
Ya ce, “Mun biya farashi mai yawa a rikice-rikicen addini a arewa, kuma ba ma bukatar yin wani abu.
Rashin tsaro da durkushewar tattalin arzikinmu ba sa nuna bambanci tsakanin Musulmai da Kiristoci.
“Muna gargadin cewa wadannan yunkurin wulakanci za su gaza, saboda ba su sami wani tallafi ba a karni tarihin da ya wuce, ko kuma a baya-bayan nan.
Yayin da muka bambanta a bin gaskiya da kabilanci, tarihi, labarin kasa da kuma abubuwan da muka samu a rayuwa a matsayinmu na ‘yan Nijeriya sun haifar da tushe na zumuncin da ba za a iya lalata su ta hanyar matsananciyar siyasa ba.
“Kuri’un Arewa za su yi tasiri sosai a zaben 2023, domin mutanenmu a yanzu sun fi kowa samun hankali da fahimta yadda za su kada su.”
Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana matasan da suka wallafa littafin a matsayin hazikan mutane da hakan ya ba shi damar goyon bayan aikin domin ganin an samu cimma nasarar gabatar da shi ga al’umma.