Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Mista Udom Emmanuel, ya ce yana nan daram a tafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ya karyata labaran da ake yadawa cewar ya bar tafiyar dan takarar.
Yayin da yake yi wa magoya bayansa jawabi a wajen taron kaddamar da takararsa ta gwamnan jihar, a Oyo babban birnin jihar a ranar Talata, inda ya ce makiya ne ke kitsa karya don cimma wata manufa tasu.
- Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Kano – FRSCÂ
- EFCC Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Aike Da Shugabanta Gidan YariÂ
“Na farka da safe na ci karo da wani labari da yake cewa na ajiye mukamina na shugaban yakin neman zaben Atiku. Wannan ba gaskiya bane, ina cikin wannan tafiya har sai mun yi nasara.
“Sun fahimci cewar mun dauki hanyar nasara ne shi ne suka fito da labaran karya don raba kawunan mutane. Kada ku saurari labaran bogi. Ina nan daram a cikin tafiyar Atiku. Babu inda zan je,” in ji shi.
Har ila yau, gwamnan ya ce nasara tana tare sa jam’iyyar PDP a dukkan manyan zabukan 2023 da ke kara karatowa.