• Leadership Hausa
Monday, March 27, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EFCC Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Aike Da Shugabanta Gidan Yari 

by Sadiq
5 months ago
in Manyan Labarai
0
EFCC Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Aike Da Shugabanta Gidan Yari 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa a jiya ya ce hukumar ta daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun birnin tarayya ta yanke na tsare shi a gidan yarin Kuje. 

Bawa ya bayyana haka ne a harabar majalisar dokokin kasar nan yayin da yake amsa tambayoyi jim kadan bayan ya gurfana gaban kwamitin majalisar kan laifuffukan cin hanci da rashawa domin kare aiwatar da kasafin kudin 2022 da kuma kudirin kasafin kudin 2023.

  • Majalisar Dokokin Adamawa Ta Amince Da Kudirin Dokar Kafa Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa 
  • An Shigar Da Manufar “Samar Da Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ga Dukkanin Bil Adama” Cikin Kudurori Uku Na MDD

“Mun riga mun daukaka kara a kan hakan don haka za mu ba da damar bin tsarin doka ya yi tasiri,” in ji shi.

A jiya ne mai shari’a Chizoba Orji na babbar kotun birnin tarayya Abuja, ya yanke wa shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta’annati (EFCC) Abdulrasheed Bawa hukuncin tsarewa a gidan yari dangane da gazawar hukumarsa na kin bin umarnin kotu.

A hukuncin da kotun ta yanke, ta ce “Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ya yi watsi da umarnin wannan kotu mai girma da ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018, inda ta umarci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, Abuja da ta mayar wa mai nema motarsa mai suna Range Rover da kuma kudi N40, 000,000 (Naira miliyan arba’in).

Labarai Masu Nasaba

Tarihin Mamayar Tattar 4

Tsokaci A Kan Mazajen Da Ke Bayyana Sirrukan Gidanjensu A Majalisa

Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ta dora alhakin hukuncin da kotun ta yanke kan wasu bayanai da ba su dace ba, inda ya ce tuni shugaban ya saki motar da ake magana a kai ya kuma amince da sakin kudin.

Tuni dai hukumar ta shiga rudani tun bayan aike da shugaban nata gidan yari.

Sai dai EFCC na ganin akwai kuskure wajen bayyana wasu bayanai wanda suke da alaka da aike da shugaban nata gidan yari.

Tags: Abdulrasheed BawaAbujaAlkaliEFCCGidan YariHukunciKotuMaitama
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yansanda Sun Damke Mutane 3 Kan Zargin Sace Wata Alkalin Kotun Majistire A Ilorin 

Next Post

Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Kano – FRSC 

Related

Tarihin Mamayar Tattar 4
Manyan Labarai

Tarihin Mamayar Tattar 4

1 day ago
Tsokaci A Kan Mazajen Da Ke Bayyana Sirrukan Gidanjensu A Majalisa
Manyan Labarai

Tsokaci A Kan Mazajen Da Ke Bayyana Sirrukan Gidanjensu A Majalisa

1 day ago
Maraba Da Azumin Ramadan Na Bana
Manyan Labarai

Maraba Da Azumin Ramadan Na Bana

2 days ago
Falalar Ramadan Da Wasu Hukunce-hukuncen Azumi
Manyan Labarai

Falalar Ramadan Da Wasu Hukunce-hukuncen Azumi

2 days ago
Matsayin Da Dimukradiyyar Nijeriya Ta Kai A Yanzu – Buhari
Manyan Labarai

Matsayin Da Dimukradiyyar Nijeriya Ta Kai A Yanzu – Buhari

2 days ago
Yadda Na’urar BBAS Ta Sauya Salon Zaben Gwamnoni
Manyan Labarai

Yadda Na’urar BBAS Ta Sauya Salon Zaben Gwamnoni

2 days ago
Next Post
Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Kano – FRSC 

Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Kano – FRSC 

LABARAI MASU NASABA

Kafar CGTN Ta Gabatar Da Jerin Bidiyo Don Yin Bayani Game Da Tsarin Demokuradiyyar Kasar Sin

Kafar CGTN Ta Gabatar Da Jerin Bidiyo Don Yin Bayani Game Da Tsarin Demokuradiyyar Kasar Sin

March 27, 2023
Kafa Dangantakar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Honduras Ya Sake Tabbatar Da Manufar Sin Daya Tak A Duniya

Kafa Dangantakar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Honduras Ya Sake Tabbatar Da Manufar Sin Daya Tak A Duniya

March 27, 2023
Gwamna Mai Barin Gado Da Zababbe Sun Fara Cacar Baki Kan Albashin Ma’aikata A Taraba

Gwamna Mai Barin Gado Da Zababbe Sun Fara Cacar Baki Kan Albashin Ma’aikata A Taraba

March 27, 2023
Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara

Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara

March 27, 2023
2023: INEC Ta Sanar Da Ranar Mika Wa Zababbun Gwamnoni Takardar Shaidar Lashe Zabe

2023: INEC Ta Sanar Da Ranar Mika Wa Zababbun Gwamnoni Takardar Shaidar Lashe Zabe

March 27, 2023
SERAP Ta Nemi INEC Ta Hukunta Gwamnoni Kan Bangar Siyasa

SERAP Ta Nemi INEC Ta Hukunta Gwamnoni Kan Bangar Siyasa

March 27, 2023
DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci

DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci

March 27, 2023
Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane

Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 5

March 27, 2023
PDP Ta Dakatar Da Tsofaffin Ministoci 2 Da Wasu 5 Kan Yi Wa Jam’iyyar Zagon-Kasa

PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa Kan Zargin Yi Wa Jam’iyyar Adawa Aiki

March 26, 2023
Amurka Ta Sake Zargin Kasar Sin Kan Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Domin Yunkurin Siyasa

Amurka Ta Sake Zargin Kasar Sin Kan Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Domin Yunkurin Siyasa

March 26, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.