Kasa da ‘yan kwanaki da babban zaben 2023, jam’iyyun siyasa guda biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 a Nijeriya, sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Jam’iyyun sun shelanta mara bayar tasu ne a yayin gangamin yakin zaben PDP da ya gudana a filin wasanni na Mahmud Ribadu da ke Yola, babbar birnin Jihar Adamawa a ranar Asabar.
- Yadda Daruruwan Dubban Jama’a Suka Halarci Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass Karo Na 37
- Tsokaci A Kan Illolin Shagwabar Da Kakanni Ke Wa Jikokinsu
Jam’iyyun sun hadar da Allied Peoples Movement (APM); African Democratic Congress (ADC); National Rescue Movement (NRM); Action Alliance (AA) da kuma jam’iyyar Action Peoples Party (APP).
Shugaban jam’iyyar APM na kasa, Yusuf Dantalle ne, ya yi magana a madadin jam’iyyun tare da mara wa takarar Atiku baya.
Ita dai jam’iyyar APM ita ce ke da mace ‘yar takarar shugaban kasa a zaben 2023, Madam Chichi Ojei, a ranar Juma’a jam’iyyar ta cimma matsayar goyon bayan Atiku a wani zaman da suka gudanar.