ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Ka Kula da Lafiyarka, Kwankwaso Ga Tinubu

by Sadiq
3 years ago
Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shawarci dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya kula da lafiyarsa gabanin shiga zaben 2023.

Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne kuma wanda ya mulki jihar Kano sau biyu, yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Lahadi, ya ce kamata ya yi Tinubu ya kula da lafiyarsa, inda ya yi gargadin cewa yakin neman zaben 2023 zai kasance da tsauri.

  • Goron Sallah: Shugaban APC Ya Yi Wa Nijeriya Addu’ar Zaman Lafiya
  • 2023: Kalubalen Tsaro Na Zama Barazana A Wasu Jihohin Arewacin Nijeriya

“Idan ka ga abokina Bola, ka ce masa ya bi a sannu, ya kula da lafiyarsa sosai… saboda ina sonsa sosai, abokina ne.

ADVERTISEMENT

“Wannan yakin neman zaben zai yi tsauri sosai, yana bukatar jajircewa sosai da dai sauransu. Ina fatan zai yi sauki domin mu ci gaba da fafutukar tabbatar da kasa daya mai karfi da wadata a Nijeriya,” in ji Kwankwaso.

Da aka tambaye shi ko Tinubu na masa barazana, Kwankwaso, wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar wakilai a jamhuriya ta uku, ya ce Tinubu a matsayinsa a kashin kansa mutumin kirki ne amma bai san abin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai yi daban da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

LABARAI MASU NASABA

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

“Damuwata kawai ita ce jam’iyyar da ya fito. Na san shi mai dabara ne, Bola Tinubu, mutumin kirki ne. Na zauna tare da shi sau da yawa ba za a iya kirgawa ba daga 1992 zuwa yau.

“Ina fatan idan gan shi zan tambaye shi me zai gaya wa ‘yan Nijeriya abin da zai yi na daban da abin da Muhammadu Buhari ke yi a yau.

“Wannan ita ce babbar damuwata a gare shi. Idan ba yi nasara ba, zan iya ba shi shawara amma zai zama kamar gina wani abu ne bai mai billewa ba.

“Idan na gan shi, zan yi masa fatan alheri ko kuma idan kun gan shi, ku ce masa ina yi masa fatan alheri – amma ya bi a sannu,” in ji Kwankwaso.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne Tinubu ya bayyana zabar tsohon gwamnan jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shetima a matsayin abokin takararsa, lamarin da ya haifar da cece-kuce a kan cancanta ko kuma rashin cancantar takarar mutum biyu data addini daya idan aka yi la’akari da kasancewar Nijeriya na da mabambamtan addinai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Siyasa

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

December 18, 2025
Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe
Siyasa

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

December 16, 2025
El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
Siyasa

El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027

December 15, 2025
Next Post
Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Kasar Amurka A Indonesia

Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Kasar Amurka A Indonesia

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.