28 ga watan Satumbar da ya gabata ne Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa ta ayyana sakin takunkumin fara yakin neman zaben Shekara ta 2023, wanda hakan ke nuni da cewa kakar zaben ta kankama.
Akan haka Gidauniyar da ke yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta Kasa YADAF Karkashin Jagorancin Shugabar Gidauniyar Hajiya Fatima Bature Jikan Dan-Uwa ta bayyana fito da wasu tsare tsaren domin dakile al’adar wasu ‘yan siyasa dake durawa matasa Kayan maye domin biyan bukatun kansu.
- Kotu Ta Yanke Wa Wani Tsoho Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Har Abada Kan Laifin Fyade A Jigawa
- Kotun Daukaka Kara Ta Umurci Kungiyar ASUU Da Ta Gaggauta Janye Yajin Aikin Da Take
Hajiya Fatima Bature JikanDan-Uwa ta bayyana Haka ne a lokacin kaddamar zagayen matattaran masu sayarwa tare ta Shan Miyagun Kwayoyi a Kano, Shirin Wanda shi ne irin sa na farko da wata kungiya ke tattalin kafa da kafa har matattarar matasa inda ake tattaunawa da su Kan dalilan da Suka jefa su cikin wannan mummunar ta’ada.
Ya ce jama’a kowa zai yi mamakin Jin dalilan wasu yaran na hakura da harkar Karatu sun gwammace afkawa cikin wannan harka ta shaye shaye.
“Wani abin mamaki da yawayaran da Gidauniyar YADAF tazanta dasu alokacin data Fara wannan zagayen kwakwaf, sun bayyana cewa Matsalar Jarrabawar Kualify ce sanadiyyar fadawa harkar Shaye-Shaye, a cewar yaran yaro yaci credit 8 Amma Gwamnati ya ce ba zata biya Masa tallafin kudin Jarrabawar ba sai abin da ya Kama daga credit 9 zuwa sama, sannan ga halin matsin tattalin arziki da ake fama dashi a kasa baki daya.
Wannan ta sa iyaye basa iya kashe wadannan makudan kudade domin biya wa yaransu Jarrabawar.
Saboda haka dole zaman Gida ya kama su,Kuma akan Haka sai ake gamuwada wasu da suka Jima a cikin harkar suna ba su shawarar Shan abinda zai rage masu wannan radadi daga nan Suka tsinci kansu a irin wannan Hali.
Hajiya Fatima Bature Jikan Dan-Uwa ta ci gaba cewa zuwa yanzu da muke wannan zagayen matattaran matasa mun sama da matasa 70 da Suka Kawo kansu domin Mayar da su makarantunsu, wannan Gidauniya ta Mayar da su tare da biya masu kudaden Jarrabawar, yanzu Haka akwai sansanin guda da tuni ya tashimatasan duk mun Mayar da su Makarantu. Ya ce  wannan na nuni da cewa zaben Shekara 2023 a Kano Babu matasa masu shaye-shaye a cikinsa, kowa ya Koma makaranta sauran Kuma tuni mun kammala Shirin bude cibiyar koyar da sana’o’i domin matasa su samu sana’ar dogaro da Kai maimakon bin ‘yan siyasar da su’ya’yansu na tura suna Karatun,mu Kuma an bar yaranmu ana takashe su ba gaira ba dalili.
Domin tabbatar da hadin guiwa da Hukumomin tsaro, Muna tunawa Hukumar zaben dokar da Gwamnati ta samar na tabbatar da gwajin kwakwalwar duk wani Mai bukatar yin takara domin tabbatar ba ya mu’amala da Miyagun Kwayoyi, ta ce a wannan gaba dole a jinjinawa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi tun a zabukan baya ya fara gwada wannan doka inda aka tabbatar da Sai da aka tura duk wani dan takara a Kano Hukumar da ke yaki da sha tare da fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA, inda aka tantace ‘yan takarkarun, har ma aka dakatar da wasu da aka samu da Matsalar shaye-shaye a cikinsu.
Ya ce yanzu haka za mu yi amfani da matasa tare da duk mai kishin ci gaban Jihar Kano da kuma masu yi wa Kano da Kasa fatan alhairi, domin bibiyar duk wani dan takara da ya nuna rashin kulawa da wannan doka ta kaucewa raba wa matasa kwayan maye a lokacin yakin neman zabe, zamu kuma bayyanawa duniya abin da muka samu kan haka, sannan zamu hada hannuda Jami’an Hukumar NDLEA domin kwarmata duk wanda ya tanadi kayan maye domin gurbata hankulan matasa.
“Sashin mu na tattaunawa da masu irin wannan matsala sun bayyana mana yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da matasa ta hanyar basu kayan maye domin samun damar cin karensu babu babbaka, saboda haka tuni wasu daga cikin ire-iren wadannan matasa sun zubar da makamansu tare alkawarin yin aiki tare da wannan Gidauniya domin ganin ba a yi amfani da matasan ba Wajen badakala a lokacin yakin neman zabe da ma lokacin Zaben ba.
Hajiya Fatima ta bayyana nasarar da wannan Gidauniyata samu daga lokacin kafuwarta zuwa yau, ta ce mun samu nasarar ziyartar Sarakuna, manyan attajirai, Jami’an Gwamnati, Malamai da limamai domin ganinmun hada hannu wajen yakar wannan babbar matsà la.
Wanda zuwa yanzu muna kara yiwa Allah godiya domin kwalliya na biyan kudin sabulu. Daga nan sai Hajiya Fatima Bature Jikan Dan-Uwa tayi amfani da wannan dama Wajen jan hankalin iyaye wajen lura da mutanen da yaransu ke mu’amala da su, domin abokai na taka muhimmiyar rawa wajen lalata rayuwar matasan wannan lokaci.
Haka ita ma tsangwama, rabuwar iyali, talauci da Matsalar rayuwar zaman aure na cikin abubuwan da ke jefa wasu matasan cikin wannan mummunan ta’ada.
A karshe Hajiya Fatima Bature ta bukaci hadin kan iyaye, Malamai, Sarakuna, Gwamnatoci da dukkan masu ruwa da tsaki domin hada hannu wajen tunkarar wannan matsala.