• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Mun Fara Horas Da Ma’aikatan Wucin-gadi Miliyan 1.2 – INEC

by Sulaiman
3 years ago
INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara aikin horas da ma’aikatan da za su yi aikin zaɓen 2023 a cikin Fabrairu da Maris.

Ma’aikatan na wucin-gadi su miliyan 1 ne da 265,227, kamar yadda Babban Jami’in Wayar da Kai kuma Kwamishina na INEC, Mista Festus Okoye, ya bayyana a ranar Litinin, a wurin bayar da wani horon a ranar Litinin.

  • CBN Ya Tabbatarwa INEC Samun Wadatattun Takardun Naira Don Gudanar Da Zaben 2023

Ya ce hukumar ta ɗauki wannan horaswa da muhimmanci, ganin cewa Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya sha alwashin tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe, karɓaɓɓe, kuma wanda jama’a za su yi tururuwar fita su jefa ƙuri’a.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Okoye ya ƙara cewa haka kuma wannan zaɓe mai zuwa, zaɓe ne wanda za a yi amfani da na’urar fasaha a wurin zaɓe.

Ya yi tsinkayen cewa aikin ofishin sa ne wanda aka ɗora wa haƙƙin shawartar Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (REC) da jami’an zaɓe hanyoyin da su ka fi dacewa su fahimtar da jama’a batutuwan da su ka danganci amfani da na’urorin fasaha a lokacin zaɓe.

INEC

Ya ƙara da cewa a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris ‘yan Nijeriya za su zaɓi shugaban ƙasa, sanatoci 109, mambobin majalisar wakilai su 360, gwamnoni 28, sai mambobin majalisar dokoki 993.

Ya ce mutum miliyan 93 da 469,008 ne su ka yi rajistar katin zaɓe, kuma ake sa ran za su fita su jefa ƙuri’a a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris.

Ya ce: “Zaɓen 2023 zai tafi ne a bisa tsarin amfani da na’urar fasahar zamani. INEC za ta yi amfani da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, wato BVAS a dukkan rumfunan zaɓe 176,846 a ƙasar nan.

“Kuma INEC ta yi gwajin waɗannan na’urorin, wato BVAS ta tabbatar da ingancin su. Yanzu haka ana ci gaba da ba su lambobin tantance mai katin shaidar rajistar zaɓe, ta yadda za su kasance lambobin sun zama mabiyi da mabiyi, ko ɗaya bayan ɗaya a lokacin zaɓe.”

A cewar Okoye, Sashen Dokar Zaɓe na 47(2) ya tilasta cewa babu wanda zai yi zaɓe ba tare da an tantance shi na BVAS ba.

Ya ƙara da cewa: “Za a yi amfani da baturen zaɓe 707, 384 da su ka haɗa da mataimakan su. Sai kuma wasu ma’aikata 17,685 a matsayin turawan zaɓe masu sa-ido, jami’an tattarawa da bayyana sakamakon zaɓe su 9,620, sai kuma jami’an tsaron rumfunan zaɓe su 530,538. Ya ce gaba ɗaya idan an haɗa, sun cika 1,265,227 kenan.

Dukkan waɗannan su na ci gaba da samun horon sanin makamar aiki, yayin da nan da ‘yan kwanaki za a ci gaba da bayar da horon ga saura, inji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 
Manyan Labarai

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya
Labarai

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Next Post
An Ciro Wata Mata Da Rai Daga Baraguzai Bayan Shafe Awa 52 A Turkiyya

An Ciro Wata Mata Da Rai Daga Baraguzai Bayan Shafe Awa 52 A Turkiyya

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.