Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

2023: Na Shiga Takarar Shugaban Kasa Ne Don Ceto Nijeriya –Gwamna Bello

by Muhammad
January 12, 2021
in LABARAI
2 min read
Bello
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ahmed Muh’d Danasabe,

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, a karshe ya fito karara ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar kujerar Shugaban Kasar Nijeriya a shekara ta 2023 idan Allah mai duka ya kai mu, inda ya ce, ya dauki aniyar tsaya wa takarar ne, domin ceto Nijeriya daga halin da ta samu kanta a ciki.

samndaads

Ya ce, ya na da abubuwa da kuma cancanta da ake bukata na samar da shugabanci nagari ga Nijeriya.

Gwamna Bello, wanda ya yi hira da Jaridar Daily Independent a ranar Lahadi da ta gabata, ya bayyana cewa, ya shiga takarar ne, don magance dimbin matsalolin da ke addabar kasar, inda kuma ya bukaci ’yan Najeriya da su mara masa baya wajen fafutukar ’yanto kasar daga kalubale daban-daban da ta ke fuskanta.

“Ina kira ga kowa ya hada hannu da ni, don ’yanto kasar nan daga halin-ni-’yasu da ta tsinci kanta a ciki. Ya zama wajibi mu yi amfani da wannan dama da muka samu wajen ganin mun ceto kasarmu,” a cewar Bello.

“Da yardan Allah, shirye nake tsaf na shugabanci Nijeriya kuma zan samar da shugabanci nagari da ake bukata a kasar nan.

“Sai dai kuma Ina kira ga ’yan Najeriya da mu yi iyakar bakin kokarinmu wajen ganin mun bai wa gwamnati mai ci yanzu a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari goyon baya a kokarin da ta ke yi na ceto kasar nan daga halin da ta tsinci kanta ciki.”

A ’yan kwanakin nan dai, akwai kungiyoyi da dama daga sassa daban-daban na Jihar Kogi da ma kasar da kuma Majalisar Dokokin Jihar suka rika kiraye-kirayen Gwamna Yahaya Bello da ya fito takarar kujerar Shugaban Kasa a zaben 2023, idan Allah ya kai mu, inda suka bada hujjarsu da cewa gwamnan mutum ne matashi, wanda ke da kudiri da kuma akidar ciyar da Nijeriya gaba, idan aka ba shi dama.

SendShareTweetShare
Previous Post

Wa Zai Gaji IGP Adamu Bayan Ritayarsa A Watan Fabrairu?

Next Post

DSS Ta Bankado Wani Shirin Tada Rikicin Addini A Nijeriya 

RelatedPosts

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

by Muhammad
9 hours ago
0

Daga Abba Ibrahim Gwale, Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince...

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Yau Za A Yi Karon Batta A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

 Jam’iyyu 11 ne za su fafata PDP Kwankwasiyya ta ce,...

Sojoji

Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci...

Next Post
DSS

DSS Ta Bankado Wani Shirin Tada Rikicin Addini A Nijeriya 

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version