Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da sabon ofishinsa na shiyyar Arewa maso Yamma.
Ofishin yakin neman zaben a Jihar Kaduna, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya bayar a matsayin gudumawa.
- Atiku Ya Tafi Turai Kan Harkar Kasuwanci
- Atiku Ya Yi Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Da Sake Farfado Da Masana’antu A Jihar Kaduna
A wajen kaddamar da bude ofishin, jam’iyyar PDP ta yabawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, bisa bayar da gudunmuwar ofishin yakin neman zaben jam’iyyar domin samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023.
Atiku ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar da suka taru a wajen bikin kaddamar da ofishin da su yi wa jam’iyyar aiki tukuru domin ganin ta samu nasara a zaben.
A cewarsa, duk wanda ya yi wa jam’iyyar aiki za a ba shi kyauta mai kyau bayan an kammala zabe.
Ya ce, “Ina son in yaba wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, bisa irin wannan karamci da ya yi wajen bayar da wannan ofishin, kowa ya yi kokari wajen ganin jam’iyyarmu ta samu nasara a zabe mai zuwa kuma ta yi nasara sosai, a wannan karon na ga hadin kan da aka samu a cikin jam’iyyar da jajircewar ‘ya’yan jam’iyyar na jihar Kaduna na kishin ganin mun yi nasarar a jihar da zaben ‘yan majalisun tarayya da na shugaban kasa.
“Ina tabbatar muku cewa jam’iyya a matakin kasa za ta ba ku goyon baya da kuma tabbatar da nasara a jiha a kowane mataki, idan kun yi wa jam’iyyar aiki da kyau kuma kuka yi wa Atiku aiki da kyau kuma ya ci zaben shugaban kasa, za a ba ku kyauta mai tsoka. .”
Tsohon mataimakin shugaban kasa Sambo, wanda ya yi magana tun farko, ya ce ‘ya’yan jam’iyyar a jihar Kaduna a shirye suke su ba Atiku gudunmawa a jihar.
Ya ce sabon ofishin da aka bayar zai zama ofishin jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Yamma da kuma jihar.
“Jihar Kaduna a shirye ta ke ta zabi PDP a zabe mai zuwa a 2023, mun riga mun yi aiki don ganin nasararku da jam’iyya a zabe mai zuwa.
“Babu shakka za mu yi nasara a wannan zabe domin kowa za a yi aiki tare domin samun nasara,” inji Sambo.
Har ila yau, a wajen taron, Amb Usman Elkudan, daya daga cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya ce wannan mafarin ne na goyon bayan da maigidansa ya yi wa takarar Atiku Abubakar.
Ya yi alkawarin za su ci zabe a kowane mataki.