ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Namadi Sambo Ya Gwangwaje Atiku Da Kyautar Ofishin Yakin Neman Zabe A Kaduna

by Muhammad
4 years ago

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da sabon ofishinsa na shiyyar Arewa maso Yamma.

Ofishin yakin neman zaben a Jihar Kaduna, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya bayar a matsayin gudumawa.

  • Atiku Ya Tafi Turai Kan Harkar Kasuwanci 
  • Atiku Ya Yi Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Da Sake Farfado Da Masana’antu A Jihar Kaduna

A wajen kaddamar da bude ofishin, jam’iyyar PDP ta yabawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, bisa bayar da gudunmuwar ofishin yakin neman zaben jam’iyyar domin samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023.

ADVERTISEMENT

Atiku ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar da suka taru a wajen bikin kaddamar da ofishin da su yi wa jam’iyyar aiki tukuru domin ganin ta samu nasara a zaben.

A cewarsa, duk wanda ya yi wa jam’iyyar aiki za a ba shi kyauta mai kyau bayan an kammala zabe.

LABARAI MASU NASABA

2027: Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Watsi Da Sukar Takarar Musulmi-Musulmi Da Kwankwaso Ya Yi

Kabiru Gaya Ya Amince Zai Sauya Sheƙa Zuwa APC

Ya ce, “Ina son in yaba wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, bisa irin wannan karamci da ya yi wajen bayar da wannan ofishin, kowa ya yi kokari wajen ganin jam’iyyarmu ta samu nasara a zabe mai zuwa kuma ta yi nasara sosai, a wannan karon na ga hadin kan da aka samu a cikin jam’iyyar da jajircewar ‘ya’yan jam’iyyar na jihar Kaduna na kishin ganin mun yi nasarar a jihar da zaben ‘yan majalisun tarayya da na shugaban kasa.

“Ina tabbatar muku cewa jam’iyya a matakin kasa za ta ba ku goyon baya da kuma tabbatar da nasara a jiha a kowane mataki, idan kun yi wa jam’iyyar aiki da kyau kuma kuka yi wa Atiku aiki da kyau kuma ya ci zaben shugaban kasa, za a ba ku kyauta mai tsoka. .”

Tsohon mataimakin shugaban kasa Sambo, wanda ya yi magana tun farko, ya ce ‘ya’yan jam’iyyar a jihar Kaduna a shirye suke su ba Atiku gudunmawa a jihar.

Ya ce sabon ofishin da aka bayar zai zama ofishin jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Yamma da kuma jihar.

“Jihar Kaduna a shirye ta ke ta zabi PDP a zabe mai zuwa a 2023, mun riga mun yi aiki don ganin nasararku da jam’iyya a zabe mai zuwa.

“Babu shakka za mu yi nasara a wannan zabe domin kowa za a yi aiki tare domin samun nasara,” inji Sambo.

Har ila yau, a wajen taron, Amb Usman Elkudan, daya daga cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya ce wannan mafarin ne na goyon bayan da maigidansa ya yi wa takarar Atiku Abubakar.

Ya yi alkawarin za su ci zabe a kowane mataki.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100
  • Muhammad
    ‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
  • Muhammad
    Cikin Shekaru 28, Kudiri Ƙasa Da 10 Sanatocin Zamfara Ta Arewa Suka Gabatar A Majalisa – Shinkafi
  • Muhammad
    2027: NNPP Ta Yi Wa Korarrun Mambobinta Afuwa, Ta Yi Alƙawarin Basu Tikitin Kai-tsaye

MASU ALAKA

Kwankwaso Zai Koma ADC Ranar Litinin
Manyan Labarai

2027: Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Watsi Da Sukar Takarar Musulmi-Musulmi Da Kwankwaso Ya Yi

July 22, 2026
Kabiru Gaya Ya Amince Zai Sauya Sheƙa Zuwa APC
Labarai

Kabiru Gaya Ya Amince Zai Sauya Sheƙa Zuwa APC

July 21, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Siyasa

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026
Next Post
Hu Hailan: Masaniyar Kasar Sin Da Ta Kai Matsayin Koli A Fannin Kimiyyar Kwakwalwa Da Jijiyoyi A Duniya

Hu Hailan: Masaniyar Kasar Sin Da Ta Kai Matsayin Koli A Fannin Kimiyyar Kwakwalwa Da Jijiyoyi A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Taron AI Na Duniya: Kaya Ya Kwance A Tushen Kaba

Taron AI Na Duniya: Kaya Ya Kwance A Tushen Kaba

July 22, 2026
Inganta Makarantu: Gwamna Lawal Ya Sanya Hannu Kan Dokokin Gyaran Ilimi A Zamfara

Inganta Makarantu: Gwamna Lawal Ya Sanya Hannu Kan Dokokin Gyaran Ilimi A Zamfara

July 22, 2026
An Kaddamar Da Taron Kasa Da Kasa Na Bunkasa Hanyar Siliki Ta Dijital Na 2026

An Kaddamar Da Taron Kasa Da Kasa Na Bunkasa Hanyar Siliki Ta Dijital Na 2026

July 22, 2026
Amit Bhatia Na Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Sayen Kaso 30 Na Liverpool FC

Amit Bhatia Na Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Sayen Kaso 30 Na Liverpool FC

July 22, 2026
Asibitin Tafi Da Gidanka Na Jirgin Ruwan Sin Ya Nufi Kasashen Afrika Da Kudancin Asiya Domin Bayar Da Hidimomin Jin Kai

Asibitin Tafi Da Gidanka Na Jirgin Ruwan Sin Ya Nufi Kasashen Afrika Da Kudancin Asiya Domin Bayar Da Hidimomin Jin Kai

July 22, 2026
Iran Ta Musanta Zargin Ɓoye Makaman Nukiliya A Dutsen Kolang

Iran Ta Musanta Zargin Ɓoye Makaman Nukiliya A Dutsen Kolang

July 22, 2026
An Kafa Cibiyar Binciken Wayewar Kai Ta Duniya

An Kafa Cibiyar Binciken Wayewar Kai Ta Duniya

July 22, 2026
Kano

Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi

July 22, 2026
Yawan Man Fetur Da Gas Da Sin Ta Samar A 2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

Yawan Man Fetur Da Gas Da Sin Ta Samar A 2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

July 22, 2026
Yaya Da Kani Sun Mutu A Cikin Ramin Masai A Kano

Uba Da ‘Yarsa Sun Mutu Bayan Faɗawa Rijiya A Kano

July 22, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.