Jigo a cikin kungiyar dattawan arewa (NEF), Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa a halin yanzu da ake ciki, manyan ‘yan takarar shugaban kasa ba za su taba iya gyara Nijeriya ba.
Ya ce a cikin ‘yan takarar shugaban kasa da ke da su a halin yanzu, gwara ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP, Mista Peter Obi da na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Masu Kwankwaso kila za su iya tabuka wani abu, amma ‘yan takatar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da na PDP, Atiku Abubakar ba za su iya tabuka komi ba.
Ya dai jaddada cewa wadannan ‘yan takara sun shafe shakara da shekaru suna gudanar da siyasa a Nijeriya ba tare da kawo wani sauyi ba. Ya ce da jam’iyyar APC ta bai wa Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo takara zai iya cewa gwara-gwara, haka ma da PDP ta bai wa tsohon ma’aikacin banki, Mohammed Hayatu-Deen takara da zai iya ganin za a samun kwarrun ‘yan takarar shugabanin kasa.
Ango Abdullahi ya kara da cewa ba zai taba goyon bayan daya daga cikin wadannan ‘yan takararan shugaban kasa ba. Ya ce yana kira ga ‘yan Nijeriya su tashi tsaye wajen kalubalantar wadannan ‘yan takarar shugaban kasa domin ganin daya daga cikinsu bai hau karagar mulki ba a 2023.
Jigon ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida ta wayar salula a cikin makon da ya gabata.
Ya ce, “Har hanzu bai ga wani dan takara da zai iya gyara Nijeriya ba. ‘Yan takarar da muka da su a yanzu ba za su iya tabuka komi ba. Domin ta yaya za a iya cewa Tinubu da Atiku za su iya gyara Nijeriya.?
“Sun kashe shekaru 25 zuwa 30 suna gudanar da harkokin siyasa, amma babu wani abu da suka taba yi na gyara Nijeriya. To me za mu yi da wadannan ‘yan takara?
“Akwai mutanen da suka cancanta amma ba su aka bai wa takara ba saboda tsarin siyasan a gurbace take,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa yana kira ga ‘yan Nijeriya da su sani akwai matsaloli a Nijeriya kuma dole su da kansu ne za su iya samar wa kansu mafita a kan wadannan matsaloli wajen zaben shugaban kasan da ya dace a 2023.