Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya sanar da cewa, za a fara shirye-shiryen Hajjin shekarar 2023 a ranar 21 ga watan Disamba.
Da yake jawabi a wajen taron masu ruwa da tsakin bayan aikin Hajji na 2022 da aka gudanar a babban masallacin kasa da ke Abuja, Hassan ya ce za a fara shirye-shiryen tsakanin NAHCON da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya a ranar.
- Kwanturola-Janar Na NIS Ya Amince Da Nadin Tony Akuneme A Matsayin Sabon Kakakin Hukumar Na Kasa
- Subul Da Bakan Tinubu: Alamu Ne Na Ba Zai Iya Shugabancin Nijeriya Ba- Dino Melaye
A cewarsa, ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki su mayar da hankali wajen yi tsare-tsare da tsaftar aikin Hajjin badi da nufin neman yardar Allah.
“Hajjin 2023 ya kusanto, ya kamata mu mai da hankali kan tsare-tsare mai kyau da kuma taka tsantsan tare da sanin cewa burinmu shi ne mu faranta wa Allah ta hanyar mahajjatanmu da suka ba da jari mai yawa da nufin bauta wa Ubangijinsu kawai.
“Bugu da kari, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, sabanin aikin Hajjin da ya gabata da aka fara shirye-shiryen a makare saboda rashin samun bayanai, ma’aikatar Hajji da Umra ta sanar da mu cewa, za a fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2023 a wani taro ta hanyar sadarwar bidiyo. wanda aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga Disamba 2022 tsakanin Hukumar Alhazai ta Nijeriya da ma’aikatar,” in ji shugaban.
Ya sanar da cewa NAHCON ta shirya gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 a kan tsarin tanadin aikin Hajji da kuma tsarin biyan kudi na yau da kullun.
“Manufarmu ta aikin Hajji 2023 ita ce kiyaye matsayin da ake da shi; wato gudanar da HSS daidai gwargwado tare da biyan kudaden da za ku je, kamar yadda aka yi na aikin Hajjin bana.”
Ya bayyana cewa taron masu ruwa da tsaki an shirya shi ne domin hada masu ruwa da tsaki a harkar Hajjin Nijeriya da nufin yin nazari tare da duba aikin Hajjin bana tare da samar da mafita don ingantawa.