Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gargaɗi jam’iyyar PDP da kada ta dawo da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, cikin jam’iyyar.
Wike ya ce dawo da Obi PDP zai zame wa jam’iyyar babbar illa.
- Xi Ya Gabatar Da Shawarar Tsarin Shugabanci Na Duniya
- AU: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Bunkasa Noma Na Da Matukar Muhimmanci
Yayin hira da ’yan jarida a Abuja a ranar Litinin, Wike ya zargi PDP da rashin ɗaukar darasi daga kura-kuran da ta yi a zaɓen 2023.
Ya ce jam’iyyar ta sha kaye ne saboda ta yi watsi da tsarin rabon mulki da adalci, inda ta bari shugaban jam’iyya da ɗan takarar shugaban ƙasa duka suka fito daga Arewa.
“Na yi gargaɗi tun farko. Ba za ku iya samun ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iyya daga yanki ɗaya ba. Na faɗa musu zai jawo mana koma baya, kuma hakan ne ya faru,” in ji Wike.
Kan batun yiwuwar Obi zai koma PDP, Wike ya yi watsi da shi, ya ce hakan zai jawo wa jam’iyyar matsala.
“Obi ya zargi PDP, ya ce jam’iyyar ta lalace. Yanzu kuma jam’iyyar ta gyara kenan a gare shi? Wannan zai kashe jam’iyyar,” in ji shi.
Wike ya ce dawo da Obi saboda kawai neman mulki zai rusa ƙa’idoji da mutuncin jam’iyyar.
Ya dage cewa hanyar da PDP za ta sake bi domin farfaɗowa ita ce bin tsarin rabon mulki, adalci da gaskiya, ta yadda shugabancin ƙasa zai koma Kudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp