‘Yan siyasa da magoya bayansu sun ci gaba da watsi da gargadin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) ta yi na gudanar da yakin neman zaben 2027.
Duk da umarnin da INEC ta bayar, siyasa tana kara yin zafi a tsakanin masu neman takara da magoya bayansu, yayin da suke kara daukar matakai na tallata burikansu da yin sharyi kan zaben 2027. Yanayin siyasa na kara zafafa a daidai lokacin da ya rage saura shekara biyu a yi zabe a Nijeriya.
Manyan ‘yan siyasa sun fara yin bayani da ke bayyana aniyarsu ta tsayawa takara, yayin da suke kuma neman goyon baya ga masu ruwa da tsaki daban-daban.
Musamman a matakin kasa, jam’iyyar APC mai mulki ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa guda daya tilo a zaben 2027, bayan samun goyon baya daga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, wato kwamitin zartarwa na kasada kuma na yankuna.
A taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 26 ga Fabrairu, 2025, APC ta amince da tazarcen Shugaba Tinubu.
A wannan rana, shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya gabatar da kudrin goyon bayan tazarcen Tinubu. Nan take tsohon gwamnan Jihar Edo da kuma dan majalisar dattawa, Sanata Adams Oshiomhole ya amince da kudirin.
Bayan wata uku, kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar APC ya bayyana shugaban kasa Tinubu a matsayin dan takarar daya tilo na shugaban kasa a zaben 2027.
Haka nan a taron kungiyar gwamnonin APC da ‘yan majalisaun tarayya na jam’iyyar sun amince da Shugaba Tinubu a matsayin dan takararsu na shugaban kasa a zaben 2027.
Kazalika, dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya tabbatar da niyyarsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, tare da alkawarin yin wa’adi guda na shekaru hudu idan aka zabe shi.
Obi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita, inda ya amsa tambayoyin daga masu goyon baya a gida Nijeriya da kuma kasashen waje. Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya yi alkawarin sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Hak kuma, tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi, ya bayyana niyyarsa ta takarar shugabancin kasa a 2027, yana bayyana kwarin gwiwar cewa zai iya kayar da Shugaba Tinubu a zaben 2027, idan ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC.
Amaechi, ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da aka yi da shi a Shafin Tuwita, ya roki jam’iyyar ADC da su ba shi tikitin takarar shugaban kasa, yana mai jaddada cewa shi ya san lagon karya Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa ta APC mai mulki.
Wani bidiyon da ake yadawa kwanan nan game da yiwuwar neman takarar shugaban kasa a 2027 na tsohon dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar. Masu sharhi da yawa sun fassara wannan bidiyon a matsayin wata alama ta nufin sake fitowa takara. Duk da haka, mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya musanta ikirarin, yana mai cewa bidiyon an dauke shi ne a 2022, kafin zaben fid da gwani na PDP.
A halin yanzu, a yankin arewa ta tsakiyar, kungiyar shugabannin matasa ta goyi bayan shahararren dan kasuwa, Dakta Gbenga Olawepo-Hashim, a matsayin dan takararsu na shugaban kasa a 2027.
Sun bayyana boyon bayan nasu ne a lokacin taron manema labarai a Abuja, wanda kungiyar matasa na arewa tsakiya (YANCP) ta shirya, ta kasance wata kungiya da ke nuna goyon bayan shugabanci ya tsaya a yankin arewa ta tsakiya a 2027.
Sashe na 94(1) na dokar zabe ta 2022, wanda ya ce jam’iyyun siyasa ba za su fara gudanar da yakin neman zabe ba a bainar jama’a har sai kwanaki 150 kafin ranar zabe kuma ba su wuce sa’o’i 24 kafin wannan ranar ba.
Babban sakataren yada labarai na INEC, Rotimi Oyekanmi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa rashin dacewa da kuma rashin bin doka ne ga kowace jam’iyya ta siyasa ta fara gudanar da yakin neman zaben 2027 a wannan lokacin, wanda hakan ya saba wa dokar zabe ta 2022.
“Babu wani tanadi na musamman a cikin dokar zabe ta 2022 da ke haramta goyon bayan ‘yan takara a wurin mutane da kungiyoyi wajen zabe.
“A karkashin sashe na 94(1) na dokar zabe ta 2022, jam’iyyun siyasa ba za su fara yakin neman zabe ba har sai ya rage saura kwana 150 kafin ranar zabe kuma za a dakata a kafin awanni 24 kafin wannan rana.
“Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba ta saki jadawalin ayyukan zaben 2027 ba, wanda zai bayyana lokacin kamfen ga jam’iyyun siyasa a fili. Saboda haka, zai zama saba wa doka ga kowace jam’iyya ta fara yakin neman zaben 2027 a wannan lokaci,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp