Rundunar ‘yansandan ƙasa da ƙasa (Interpol) tana neman ‘yan Nijeriya 14 ruwa a jallo bisa zargin aikata laifuka daban-daban, waɗanda suka haɗa da sata, zamba, da safarar miyagun ƙwayoyi.
Sanarwar da aka fitar a shafin intanet na Interpol ta nuna cewa waɗannan mutane ana tuhumar su ne daga ƙasashe daban-daban da ke neman su saboda ayyukan laifi da suka aikata.
- Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Goge Munanan Abubuwan Da Suka Shafi Kasar Sin A Cikin Kudurin Manufofin Tsaro Na Shekara-shekara
- Sanata Barau Ya Roƙi Ganduje Ya Ƙwato Jihohin Da Suka Yi Wa Jam’iyyar APC Tutsu
Daga cikin waɗanda aka bayyana sunayensu akwai Felix Omoregie, Jessica Edosomwan, Uche Egbue, Jude Uzoma, Chinedu Ezeunara, Benedict Okoro, Ikechukwu Obidiozor, da Alachi Stanley.
Sauran sun haɗa da Bouhari Salif, Timloh Nkem, Austine Costa, Okromi Festus, Akachi Vitus, da Mary Eze.
Interpol ta ce ana ci gaba da neman waɗannan mutanen domin gurfanar da su a gaban shari’a kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp