Wani sabon rigima ya sake barkewa a tsakanin kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) da kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami dangane da fara zabtare bashin dala miliyan 418 na tallafin Paris Club da gwamnonin suka karba.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa a shekarun baya ne dai gwamnatin tarayya ta shiga asusun ajiyar kudin tallafin Paris Club inda ta ciro dala miliyan 418 gami da baiwa gwamnonin Nijeriya su 36 a matsayin rance ko bashi sakamakon matsalolin da jihohin ke fuskanta da suka hada da matsalar tattalin arziki, biyan albashi da fansho saboda karancin kudi da ake fuskanta da kuma faduwar darajar mai a kasuwannin duniya a wancan lokacin.
Tun lokacin da gwamnatin ta fara shirye-shirye da bukatar gwamnatocin da su dawo da kudaden tallafin Paris da suka ci, nan kuma suka kekashe kasa suka ce atafau ba za a cire musu kudin ba.
Wakilinmu ya labarto cewa rikicin na da alaka ne da umarnin da Ministan Shari’ar kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubukar Malami ya bayar na biyan wani bangaren na kudin ga kwararrun da suka shiga tsakani domin kungiyar Paris Club ta yafe wa kasar bashin da ta ciyo daga hannunta a shekarun da suka gabata.
Sai dai gwamnonin jihohi 36 a karkashin inuwar kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) sun caccaki Abubakar Malami kan wannan mataki saboda a cewarsu batun na gaban kotu.
Sabowar takaddamar ta kunno kai ne a makon nan sa’ilin da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce yunkurin zabtare kudaden daga asusun gwamnatocin babu fashi, inda kuma kwararru na musamman da ke aiki kan maido da kudaden Paris Club sun soki kungiyar gwamnonin da yin karya kan batun kudaden na Paris Club.
Shi dai ministan shari’a Abubakar Malami ya shaida cewar babu ta yadda gwamnonin za su yi su hana zaftare kudaden Paris Club na dala miliyan 418 da suka amsa.
Ya ce, tun farko gwamnonin su ne suka janyo ‘yan kananun magana kan batun wanda kuma ya nuna hakan da cewa bai dace ba.
Gwamnonin dai sun cewa ba su yarda a fara zaftare musu kudade da sunan Paris Club ba domin kuwa kes din na gaban kotu kuma yin hakan bayan magana na gaban kotu saba doka ne.
Matsalar dai ta shiga tsakanin bangarorin uku shi ne batun biyan kwararru da kuma ganin da gwamnonin suke yi na cewa ba yanzu ne ya dace a fara zaftare kudaden ba.
Malami ya kara da cewa, kwararrun ne suka kai karar gwamnoni zuwa kotu kuma sun nemi yin sulhu inda kotu ta amince da hakan. Malami ya ce, sun cika sharuddan sasantawar a rubuce kuma gwamnonin sun amince a bai wa kararru kaso daidai da yadda suka sanya hannu.
“Gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta bukaci fara aiwatar da biyan. Kuma shugaban kasa ya umarci ofis din ministan shari’a da ya duba batun.”
Malami ya nuna cewa bayan hakan gwamnati ta bi matakan da suka dace wajen bibiyar yadda za a maido da kudaden kana sun yi shirin fara zaftare kudaden amma gwamnonin na ta kawo cikas.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Abuja, babban kwararre kuma mashawarci kan lamarin kudin Paris Club, Mista Ned Nwoko, ya zargi gwamnonin da karban dala miliyan 100 da farko. Kana daga baya lokacin da aka gabatar da kudirin dala miliyan 350 a matsayin tuntuba, gwamnonin sun bukaci a basu kashi 50 cikin dari kafin.
A cewarsa ma’aikatar shari’a ta shiga tsakani inda gwamnonin suka samu nasarar karban dala 100.
Ya kara da cewa, su kwararru basu da wata alaka da dala miliyan 418 da gwamnoni suka karba.
Ya kuma wanke Ministan Shari’a Abubakar Malami, tare da cewa babu wani abun da ya yi illa kokarinsa na ganin an bi doka.
Nwoko ya ce yarjejeniya da ka’idojin da aka shimfida kan kudaden na Paris Club sun gudana ma tun kafin zuwan gwamnatin Buhari, don haka a cewarsa bai dace kuma yanzu da aka fara maganar maido da kudaden gwamnonin su daga jijiyar wuya ba.
Babban kwararren ya zargi shugaban kungiyar gwamnoni Kayode Fayemi da shararar karya dangane da biyan kudaden ga kwararrun mashawartan.
Sai dai gwamnonin sun nuna cewa kalaman da aka danganta da Malami cike suke da son kai da karya, kana sun ce ba su ki ko yin adawa da cire dala miliyan 418 na maida kudaden Paris Club ba, sabanin yadda Malami ke kokarin nunawa na cewa sun ki amincewa a fara zaftare kudin ne.
Gwamnonin sun yi batun cewa dukkanin kalaman da ministan shari’an ya yi karya ce, sun bigi kirji da cewa a ci gaba da tafka shari’a daga nan har zuwa kotun koli suna nan a kan gaskiyarsu.
A wata sanarwar da gwamnonin suka fitar dauke da sanya hannun daraktan yada labarai na kungiyar gwamnoni (AGF), Abdulrazakue Bello-Barkindo, ya ce gwamnonin ba su ma da lokacin batawa wajen kare kansu daga irin wanna zargin marar tushen.
A cewar gwamnonin, muddin shi Ned Nwoko na da gaskiya kan maganganunsa me zai hana shi ya bi hukumomin da suka dace wajen daukan matakin shari’a kan kowaye da ake ganin ya shiga an dama da shi wajen karkatar da kudaden.
Ita ma dai kungiyar na gwamnonin sun zargi shi Nwoko da yin karya da kokarin rufe gaskiyar abubuwan da suke akwai tare da batutuwan da suka shafi shari’a hadi da shigo da wasu batutuwan da ba haka suke ba domin rufe gaskiyar.
Gwamnonin sun ce muddin ma akwai karkatar da kudaden Paris Club din, to kuwa ba wai ta hanyar fitar da jawabai na manema labarai ne za a shawo kan matsalar ba, sun ce muddin kwararrun na da gaskiya su na iya daukan matakan shari’a domin tabbatar da kowa ya bi doka.
Gwamnonin sun kara da cewa ba ma su da lokacin da za su tsaya suna batawa wajen amsa irin wannan batutuwan, to amma domin wanke kai daga karyan da aka shigar wa jama’a ne suka dacewar fitowa su ware batun.
Barkindo ya kalubalanci kwararrun da cewa su dakata har sai sun yi nasara a shari’ar da suke yi kafin daga bisani su nemi dawo musu da kudaden.
Gwamnonin sun nuna shakkunsu kan yadda ministan ya yanke ta goyon bayan a biya su dala miliyan 418 daga asusun gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi. Sun kuma zargi ministan da alaka da kwararrun.
A shekarar 2005 ne kasashen duniya masu bayar da bashi karkashin Kungiyar Paris Club suka yafe wa NIjeriya bashin da suke binta.
Kasashen sun yi haka ne domin Kasar ta yi amfani da kuDin don samar da ababen more rayuwa ga al’ummarta.
Kudin da ake zargin kwararrun suna bin gwamnati kan aikin da suka yi lokacin tattaunawar neman kungiyar Paris Club ta yi wa Nijeriya yafiya, sh ya kasance tushen takaddama tsakanin bangarorin gwamnati uku.
Idan za ku iya tunawa ma dai a watan Maris din da ta gabata wata babbar kotu a Najeriya ta yi watsi da bukatar Gwamnonin Nijeriya 36 na hana gwamnatin tarayya zabtare bashin dala miliyan 418 da ta basu daga asusun Paris Club domin magance matsalolin da suka addabe su.
Mai shari’a Inyang Ekwo da ke jagorancin kotun Abuja ya bayyana karar da gwamnonin suka shigar a matsayin mara tasiri wanda ya ce wani yunkuri ne na bakawa kotu lokaci.
Gwamnonin 36 ta hannun lauyan su Sunday Ibrahim sun bukaci kotu ta dakatar da gwamnatin tarayya daga zabtare bashin da ake bin su na Dala miliyan 418 daga asusun ajiyar su da ake zuba musu arzikin kasa.
Kafin wannan lokaci, kotun taki amincewa da wata bukata na dakatar da gwamnatin tarayyar daga taba kudaden jihohin har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.