Wata masaniyar aikin likitanci ‘yar asalin Jihar Bauchi da ke zaune a Birnin Tarayya Abuja, Dakta Maryam Almustapha ta warware tunanin da jama’a da dama ke yi na cewa matsalar Dannau a lokacin tashi daga bacci aljanu ne ke haifar da shi, wanda ake ganin kamar aljanu ne ke danne mutum, tana mai nuni da cewa matsala ce da kwakwalwa ke haddasawa.
A hirar da ta yi da jaridar LEADERSHIP, Dakta Maryam ta bayyana cewa matsalar Dannau tana sanya mutum ya kasa motsi a lokacin da ya farka daga bacci, wanda hakan kai tsaye aikin kwakwalwa ne da tsokokin jiki (Muscles).
Ta ce matsalar wacce take iya firgita wanda ya samu kansa a ciki, ta kan saka mutum ba kawai ya kasa motsi ba, har ma ya gagara numfashi duk da cewa yana farke a gadonsa kuma yana cikin hankalinsa.
“Matsala ce da ta kan auku ga mutane da yawa wacce kan sa mutum ya kasa motsi, yin numfashi da kuma gane-gane da jiye-jiye”, in ji ta.
Ta ce matsalar za ta iya faruwa ga mutum kafin ya yi bacci ko bayan ya farka kuma za ta iya daukar dakikoki ko wasu mintuna kafin ya saki mutum, tana mai karawa da cewa Dannau ya zamo ruwan dare cikin al’umma yadda in ka samu mutum 100, akalla mutum hudu su kan fuskanci matsalar daga lokaci zuwa lokaci.
Dadin dadawa, Dakta Maryam ta ce bacci ya kasu kashi biyu; da bacci mai nauyi da ake kira da ‘REM sleep’ da mara nauyi wanda ake kira da ‘non REM sleep’ a turance.
Masaniyar aikin likitancin ta cigaba da cewa a lokacin bacci mai nauyi ne mutane suke mafarki wanda yake sanya kwakwalwa ta kashe tsokokin jiki don hana mutum ya buga jikinsa ko kuma ya fado kasa daga gado sakamakon motsawar jikinsa lokacin da yake mafarki.
Maryam ta ce matsalar Dannau ta kan faru ne idan kwakwalwa ta ki kunna tsokokin jiki don su cigaba da motsi bayan mutum ya farka daga bacci, sannan kuma ba a gano hakikanin abin da yake janyo matsalar Dannau ba lokacin farkawa daga bacci.
Sai dai ta ce wasu daga cikin abubuwan da suke janyo matsalar sun hada da mutum ya yi bacci a kan bayansa, rashin yin bacci akai-akai, shan giya da sauran kayan da suke sa maye, yin gadon matsalar daga dangi, gajiya, damuwa, da tsoro za su iya haddasa ta.
Da take bayyana cewa Dannau baya da magani, akwai abubuwan da in mutum ya kiyaye zai guje wa fuskantar matsalar.
Abubuwan sun hada da daina kwanciya ta baya, kauracewa wa shan giya, yin bacci akai-akai, yin bacci lokacin da ka saba yi, samun isasshen bacci kamar awa shida zuwa takwas ko wace rana, kashe wuta da rage sauti mai hana bacci lokacin da mutum zai kwanta.